Fada Ya Ɓarke tsakanin Ƴan Sanda da Dakarun Amotekun, An Yi Harbe Harben Bindiga
- Rikici ya barke a Akure, birnin jihar Ondo tsakanin jami’an Amotekun da ’yan sanda kan wani da aka kama bisa zargin satar kayan coci
- Yayin rikicin, an ce jami'an Amotekun sun yi harbe-harbe, lamarin da ya tayar da hankulan mutane da kuma martani daga 'yan sanda
- Daga baya, hukumomin tsaro sun sulhunta lamarin, inda aka mayar da wanda ake zargi da kayan satar ga ’yan sanda daga hannun Amotekun
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Rikici ya barke tsakanin jami'an tsaron Amotekun da dakarun 'yan sanda a jihar Ondo kan wani mai laifi da aka kama.
An ce jami'an Amotekun da na 'yan sanda sun yi arangama a Akure, babban birnin Ondo a ranar Lahadin karshen makon da ya gabata.

Source: Twitter
'Yan sanda da Amotekun sun kacame a Ondo

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Boko Haram ta kashe sojoji 4, ta kona dakin ajiyar makamai a Yobe
Jaridar The Cable ta rahoto cewa ana zargin wanda aka kama da laifin satar kayan wani coci da ke kusa da tashar mota ta Sunday BS, a kan titin Ijoka a Akure.
Sabani tsakanin ɓangarorin biyu ya haifar da harbe-harben bindiga, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin, inda mutane suka fara gudu don tsira da rayuka.
Rigimar ta ƙara tsananta ne a kusa da filin ShopRite da ke daf da hedikwatar Amotekun, da misalin ƙarfe 2:00 na rana.
Jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sanda a jihar, Olusola Olayinka, ya bayyana cewa ’yan sanda ne suka isa wurin da lamarin ya faru kafin sauran jami'an tsaro.
Matsayar 'yan sanda kan rikicinsu da Amotekun
Olusola Olayinka ya zargi jami’an Amotekun da karɓe wanda ake zargi tare da sauran hujjoji da karfi da yaji, lamarin da ya kai ga jikkata ɗaya daga cikin ’yan sanda.
Olusola Olayinka ya ce:
“Da misalin karfe 8:00, an samu rahoton kama wani da ake zargin ya saci kaya a wani coci kusa da tashar motar Sunday, wanda aka miƙa rahotonsa ga ofishin ’yan sanda na Ijoka.
“DPO ya tura jami’ansa uku zuwa wurin don karɓo wanda ake zargin tare da kayayyakin da ake zargin ya sata domin adana hujjoji.”
Jami'in 'yan sanda ya ce yayin da ma'aikatansu suke gudanar da aikinsu, sai jami’an Amotekun suka iso tare da gungun masu okada, wanda hakan ya haifar da rikici.

Source: Facebook
Amotekun sun fusata, sun yi harbe-harbe
Biyo bayan haka, kwamishinan ’yan sanda na jihar, Wilfred Olutokunbo Afolabi, ya ba da umarnin a dawo da a kai masa wanda ake zargin da kuma kayan da aka sace.
Bayan wani zaman sulhu tsakanin jagororin hukumomin biyu, an mayar da wanda ake zargi da kayan satar zuwa hannun ’yan sanda.
Sai dai Olayinka ya ce wasu daga cikin jami’an Amotekun sun fusata da wannan mataki na mika wanda ake zargin, inda suka fara harba bindiga a iska.
A cewarsa, domin hana rikici da take doka, ’yan sanda sun mayar da martani ta hanyar harba borkonon tsohuwa, ba tare da musayar wuta ba.
Jami'an Amotekun sun kama 'yan Arewa 63
A wani labari, mun ruwaito cewa, jami’an Amotekun a jihar Osun sun cafke 'yan Arewa 63 da suka boye a cikin wata babbar mota cike da dabbobi da babura.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da neman hatsabibin ɗan bindiga Bello Turji, yaransa sun yi ta'asa a Sokoto
Direban motar, Salisu Ahmed, ya bayyana cewa sun taso daga Gombe zuwa Legas, amma ya kasa bayyana dalilin da ya sa mutane ke boye a cikin motar.
Shugaban Amotekun na Ondo, Cif Adetunji Adeleye, ya ce an gano babura 10 masu rajista da sunan Yarbawa da kuma 15 da ba su da rajista.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
