Amotekun ta kama 'yan arewa 63 cikin shanu da babura a bayan babban mota a Osun

Amotekun ta kama 'yan arewa 63 cikin shanu da babura a bayan babban mota a Osun

  • Jami'an tsaro na Amotekun a Jihar Osun sun kama wasu mutane 63 sun boye cikin babban mota makare da dabbobi da babura
  • Direban motan, Salisu Ahmed, ya ce sun taso daga Gombe ne za su Legas amma ya kasa bayani game da mutanen da aka gano sun boye a bayan motar
  • Cif Adetunji Adeleye, shugaban Amotekun na Ondo, ya ce sun gano babura 10 masu rajista da sunan Yarbawa da kuma 15 marasa rajista

Ondo - Jami'an hukumar tsaro da Amotekun reshen Jihar Ondo, ta kama wata babban mota a Iju, karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar, dauke da maza kimanin 63 daga arewacin Najeriya sun boye a ciki.

Baya ga mutanen, an kuma loda wa babban motar shanu, raguna da babura yayin da mutanen suka boye cikin dabobin da baburan a cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Yan ta'adda a Kaduna sun datse wa mutane 2 gaɓoɓi, sun sace 22 sun kuma raunata 4

Amotekun ta kama 'yan arewa 63 cikin shanu da babura a bayan babban mota a Osun
Jami'an Amotekun a Ondo sun kama 'yan arewa 63 cikin shanu da babura a bayan trela. Hoto: Tribune
Asali: Twitter

An tattara bayanai cewa mutanen sun yi ikirarin sun taso daga garin Gigawa ne a Jihar Gombe suna hanyar zuwa Legas kafin a tsare su sannan jami'an jihar suka kama su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Salisu Ahmed, direban motan mai lamba 'Kano AB 234 BDJ' ya ce suna hanyarsu ta zuwa Legas ne amma ya kasa yin bayani dangane da mazan da suka boye a motar.

Shugaban Amotekun na Osun ya magantu

Kamar yadda jaridar ta rahoto, babban kwamandan Amotekun na jihar, Cif Adetunji Adeleye ya ce:

"Jami'an mu suna aikinsu ne yayin da suka ga trela makare da babura da shanu.
"An kama su a kan hanyar Iju, yayin da ake bincika motar aka gano ba raguna da babura kadai suka dako ba amma akwai mutum 63, babura 10 masu rajista da sunan yarbawa, 15 marasa rajista da kuma shanu 240."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

Ana daf da yanka su: Amotekun sun ceto makiyaya fulani 2 da wasu fulanin suka yi garkuwa da su

A wani labarin, hukumar tsaro ta jihar Ondo da ake fi sani da Amoketun Corp, ta ceto Fulani makiyaya biyu da 'yan uwansu makiyaya suka yi garkuwa da su, The Punch ta ruwaito.

Wasu gungun masu garkuwa da mutane ne suka sace makiyayan a Supare Akoko, karamar hukumar Akoko kudu maso yammacin jihar kwanakin baya.

Kwamandan hukumar a jihar, Cof Adetunji Adeleye, ya bayyana sunayen wadanda aka ceto din - Musa Ibrahim da Amidu Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel