Yan acaba sun yi kone kone a ofishin Yansanda saboda suna kwace musu kudi

Yan acaba sun yi kone kone a ofishin Yansanda saboda suna kwace musu kudi

Wasu gungun fusatattun yan acaba sun yi zuga zuwa ofishin yansandan Najeriya dake garin Zuba na jahar Neja, inda suka banka ma ofishin wuta tare da kona motocin da yansandan suke amfani dasu wajen gudanar da sintiri.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan acaban sun dauki wannan mataki ne bayan cin zarafin guda daga cikinsu da Yansandan suka yi saboda yaki amincewa ya basu kudi, inda yan acaban suka ce sun gaji da cin zalinsu da Yansandan suke yi suna kwace musu kudi.

KU KARANTA: Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Yan acaba sun yi kone kone a ofishin Yansanda saboda suna kwace musu kudi

Yan acaba sun yi kone kone a ofishin Yansanda saboda suna kwace musu kudi
Source: Facebook

Wannan lamari dai ya auku ne da misalin karfe 8 na safe zuwa karfe 10 na safiyar Alhamis, 23 ga watan Mayu, wanda hakan ya janyo zaman dar dar da tashin hankali a yankin, tare da gurgunta hada hadar kasuwanci don tsoron abinda kaje ka dawo.

Wani dan Achaba dake yankin yace “Yansanda sun sha tare yan acaba suna kwace mana kudi, sun mayar damu tamkar na’urar ATM da take basu kudi a duk lokacin da suka ga dama, don haka muka dauki alwashin ba zamu lamunci wannan cin zali ba, sai dai su kashemu,”

Shima kaakakin Yansandan babban birnin tarayya Abuja. DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da kai harin tare da kona ofishin Yansandan, inda yace tuni sun kaddamar da bincike akan lamarin, tare da burin kama duk masu hannu a ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel