Lakurawa Sun Sauya Salon Ta'addanci, Sun Hallaka Sama da Mutane 10 a Sokoto
- Mafarauta 13 ake fargabar sun mutu a jihar Sokoto, bayan sun fada cikin komar ‘yan ta’addan Lakurawa da ke ta'addanci a Talewa
- Wani mazaunin yankin Tangaza, ya shaida cewa sama da mafarauta 10 ne aka neme su aka rasa bayan wannan mummunan farmaki
- Jami'an gwamnari sun ce Lakurawa sun sauya salon hare-harensu, yanzu sun koma farmakar sojoji tare da satar dabbobin mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Aƙalla mafarauta 13 ake fargabar sun mutu bayan da wasu da ake zargin 'yan ta’addan Lakurawa ne suka farmake su a Sokoto.
An ce 'yan ta'addan Lakurawa sun farmaki mafarautan ne a dajin Hurumi, gundumar Talewa, ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Source: Twitter
Ana fargabar Lakurawa sun kashe mafarauta 13
Jaridar Daily Trust ta gano cewa mafarautan, da suka fito daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa, sun gamu da hare-haren ne a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin Tangaza ya shaida wa jaridar cewa mafarautan, suna ɗauke da bindigogin gargajiya da karnukansu, inda suka yi kuskuren fadawa komar 'yan bindigan.
“Mun samo gawarwaki uku yanzu haka, amma ba a san inda mutum 10 suke ba. Wasu da suka tsira sun koma gida,” in ji wani mazaunin yankin.
Wasu mazauna yankin sun ce garin Kangiye ya rasa mafarauta biyar, Chancha da Rantijadi sun rasa biyu-biyu, Gidan Kaji da Gandaba Yamma sun rasa ɗaya-ɗaya, sannan Gandaba Gabas ta rasa biyu.
Sojoji sun dakile hari, Lakurawa sun lalata turken MTN
A ranar Juma’a, wasu da ake zargin mayakan Lakurawa suka kai hari na daban a kauyen Magonho da ke Tangaza, amma sojoji sun dakile harin, tare da kwato dabbobi.
Sai dai bayan awa biyu, ‘yan bindigar sun dawo garin, inda suka tarwatsa turken sadarwar MTN da bam, wanda ya katse layin sadarwa a yankin baki ɗaya.
Wani jami’in gwamnati daga karamar hukumar Tangaza ya ce ‘yan bindigar sun tsara amfani da farautan don janyo sojoji cikin tarkonsu.
“Ba wai mafarauta ne a gaban Lakurawa ba. Sojoji ne suke so su kashe, don haka ne suka shirya amfani da mafarautan a matsayin tarko,” in ji jami’in.
Ya ce bayanan sirri da jami’an tsaro suka tattara ne suka hana sojoji zuwa wurin mafarautar a ranar da lamarin ya faru.

Source: Original
Lakurawa sun sauya dabarun hari a Sokoto
Jami'in gwamnatin ya kara da cewa:
“Sun daina kakaba dokokinsu a kan garuruwa kamar yadda suka saba. Yanzu sun koma satar dabbobi da farmakar jami’an tsaro. Sannan suna kwace makamai a hare-harensu."
An ce sun dasa nakiyoyi a hanyoyin da ke kaiwa sansanoninsu don kare kansu daga hare-haren gwamnati.
“Babu ƙauye a Tangaza da ba su shiga ba, sai dai Masallaci da Rakah inda aka girke sansanonin soja. Amma sun karbe ikon gundumar Salewa gaba ɗaya,” inji jami’in.
Asalin Lakurawa da zuwansu Najeriya
A wani rahoton Legit Hausa na musamman, an ji cewa, an kafa kungiyar Lakurawa a 1997 a ƙarƙashin Shuga a Ibrahim Baré Maïnassara na Jamhuriyar Nijar domin kare makiyaya daga barayin shanu.
Domin tunkarar 'yan fashi masu mugayen makamai, an ba su horon soja tare da kayan yaƙi na zamani, sannan aka buɗe sansaninsu na farko a Ekrafane.
Bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a Libya a 2011, wasu daga cikin Lakurawa suka watse zuwa Mali da Arewacin Najeriya, suka shiga tada tarzoma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

