Faɗan Daba: Ɗan Siyasa Ya Haɗa kan Matasa da ba Su ga Maciji a Kano, an Samu Mafita
- Matasa da kungiyoyi masu gaba da juna sun taru a Kano domin samar da zaman lafiya da yaki da miyagun kwayoyi a cikin al'umma
- Abdulkareem Abdussalam Zaura ya ce an fitar da shirin domin ganin Kano ta samu kwanciyar hankali ba tare da rikici ba
- An kafa kwamitin mutum 20 domin gano dalilan rikicin matasa, da tallafa musu ta hanyar koyar da sana’o’i da dawo da su makaranta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu kungiyoyin matasa da suka hada da yan daba, ’yan banga da mafarauta sun taru a Kano domin dakile tashin hankali a sassan jihar.
Wannan yunkuri yana da nufin kafa wata manufa ta zaman lafiya ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, wanda ya mayar da hankali kan jama’a.

Source: Twitter
An yi taro kan fadan daba a Kano
Wanda ya shirya taron shi ne fitaccen dan siyasa kuma mai bayar da tallafi daga Kano, Abdulkareem Abdussalam Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaura ya ce wannan taron na nuna “ruhin Kano” ne wato kishin zaman lafiya ba tare da siyasa ko wariyar yanki da tashin hankali ba.
Yayin da yake magana da manema labarai game da wannan shiri, ya ce:
“Wannan aiki ne da na dade ina shiryawa, na daga cikin tsarin siyasa ta.
“Dukkanmu muna da buri daya ganin Kano ta samu zaman lafiya. Babu Daba, babu fada tsakanin kungiyoyin matasa da mafarauta."
Zaura ya ce kowane mutum da ke taron yana da dubban magoya baya, kuma hadin kansu na da matukar tasiri wajen wanzar da zaman lafiya.
Al’adar faɗan Daba a Kano na da nasaba da tashin hankali, amfani da miyagun kwayoyi da kuma laifuka kanana, wanda ke damun al’umma.
A cewarsa, taron zaman lafiyar ya hada shugabannin Daba da ’yan banga domin samun fahimtar juna da daukar mataki tare.

Source: Facebook
Fadan daba: An kafa kwamiti na musamman
Taron ya kare da kafa kwamitin mutum 20 da zai rika tuntubar shugabannin matasa a kowane sashe na jihar Kano.
Kwamitin ya fara aiki, inda ake sa ran zai gano musabbabin rikicin matasa, da samar da mafita da dawo da wadanda suka kauce hanya.
“Muna da shirin koya sana’a ga masu niyya, da dawo da wadanda suka daina makaranta, da taimaka wa wadanda ke da sana’a ba tare da jari ba.”
- Cewarsa
Ya ce, kwamitin yana samun goyon baya daga shugabannin al’umma da masu tasiri, wasu ma sun fara kiran mabiyansu da su guji tashin hankali.
Yan sanda sun hallaka ɗan daba a Kano
Kun ji cewa Jami'an ƴan sanda a jihar Kano sun kawo ƙarshen ayyukan ta'addancin wani tantirin ɗan daba da ake kira Baba Beru.
Yan sandan sun hallaka Baba Beru ne bayan ya yi yunƙurin farmakarsu da wuƙa lokacin da suke je kama shi a jihar Kano.
Baba Beru dai ya gamu da ajalinsa ne a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025 a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano.
Asali: Legit.ng

