Ogun: Tinubu zai Bude Kamfanin Auduga Mafi Girma a Duniya, Za a Samu Ayyuka
- Rahotanni na nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu zai kaddamar masana'antar sarrafa auduga mafi girma a duniya a jihar Ogun
- Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tabbatar da cewa kamfanin zai rika samar da ayyukan yi ga mutane 250,000 a jihar
- Bayanin da gwamnatin Ogun ta yi ya nuna cewa an zabi kafa kamfanin a Iperu/Ilisan saboda saukin samun kayan aiki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya sanar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da aikin gina babbar masana'antar sarrafa auduga mafi girma a duniya a jihar.
Za a gina masana'anta ne a ƙarƙashin shirin bunkasa noman auduga na gwamnati a yankin da ake noma a jihar musamman a kusa da filin jirgin sama na Gateway a Iperu/Ilisan.

Kara karanta wannan
Uwar Bari: Fubara zai kara zama da Wike a shirin sulhu a Rivers, APC da PDP sun magantu

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda za a kaddamar da kamfanin ne a cikin wani sakon da gwamnatin jihar Ogun ta wallafa a shafinta na X.
A cewar Gwamna Abiodun, aikin zai shafi filin da ya kai hekta 400, kuma ana sa ran za a samar da kusan ayyukan yi 250,000 a kullum daga masana'antar.
Dalilin kafa kamfanin auduga a Ogun
Gwamna Abiodun ya bayyana cewa an zabi yankin Iperu/Ilisan ne don kasancewarsa mai saukin samun kayan aiki da kuma kasancewar yana da hanyoyi, asibitoci da makarantu.
Ya kara da cewa gwamnati na ci gaba da gina muhimman hanyoyi da gine-gine a yankin domin tabbatar da cewa masana'antar za ta ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba.
Kazalika, ya bayyana cewa rundunar sojin sama ta Najeriya za ta kafa sansani a yankin domin tabbatar da tsaro da kare dukiyoyin masu zuba jari da ma’aikata.
Za a samu aiki a kamfanin audugan Ogun
Gwamnan ya ce wannan gagarumin aiki zai sauya tattalin arzikin jihar Ogun da ma Najeriya baki ɗaya, duba da yadda za a samar da dubban ayyukan yi ga matasa.
Ya kuma yabawa tsohuwar Akanta Janar ta Tarayya, Oluwatoyin Madein, bisa irin gudummawar da ta bayar ga ci gaban jihar Ogun, musamman a fannin kudi da tsare-tsare.
Shugabannin gargajiya da na siyasa a yankin Iperu sun bayyana jin dadinsu bisa wannan ci gaba da suka samu.

Source: Twitter
Sun bayyana cewa yankin ya rikide zuwa babban birni mai cike da sababbin gine-gine da abubuwan more rayuwa a yanzu haka.
A cewar su, masana’antar za ta kara haskaka jihar Ogun a idon duniya tare da jawo hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya.
Tinubu ya bude ayyuka a jihar Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya ya kai ziyarar aiki jihar Katsina domin bude wasu ayyuka da gwamna Dikko Umaru Radda ya yi.
Bola Tinubu ya bude wani babban titi da aka yi a jihar Katsina tare da wata cibiyar habaka noma da aka samar.
Gwamnatin jihar Katsina za ta yi amfani da damar wajen isarwa Bola Tinubu damuwowinta, musamman kan tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

