Jihohi 6 da suke cin moriyar tattalin arziki
Hukumar fitar da alkalumma ta kasa (NBS) tace tattalin arzikin kasa ya karye da kashi 0.36, karancin matsayin daya taba kaiwa kenan a shekaru 25.
Sai dai duk da lalacewar tattalin arzikin, akwai wasu jihohin da matsalar ba zata tagayyara su ba sosai, jihohin suna da karfin da zasu iya zama da kan su sakamakon yawan kudin shigan da suke samu, ba tare da sun jira rabon daga asusun gwamnatin tarayya ba. Garuruwan sun hada da:
Jihar Legas nada yawan al’umma da suka kai miliyan 20, sa’annan itace jihar da tafi samun kudaden shiga da suka kai naira biliyan 268.23 a shekara. Bugu da kari, gano arzikin man fetur da aka yi a jihar ya kara mata kudaden shiga, ta hanyar cancantar samun kashi 13 da ake baiwa jihohi masu arzikin man fetur. Jihar Legas zata iya cigaba da tafiyar da harkokin jihar sakamakon kasancewarta tushen hada hadar kudi na kasar nan.
Gwamnatin jihar Imo tayi kokarin karkata akalar tattalin arzikin jihar daga man fetur zuwa fannin ma’adanin kasa, duk da cewa tana da tarin arzikin man fetur. Sa’annan habbaka noma da jihar tayi ya taimaka wajen samar mata da karin kudin shiga.
Duk da cewa jihar Bayelsa na daya daga cikin jihohin da suka fi samun kaso mai tsoka na kudade daga asusun gwamnatin tarayya, tare da mallakar arzikin iskar gas da na man fetur, amma itace jiha mafi karancin al’umma a Najeriya. Ga shi kuma jama’ar kasar na harkar kiwon kifi.
KU KARANTA:Matsalar Tattalin Arziki: Za mu taimakawa Kasar Najeriya-UN
4.Kano
Jihar Kano itace jiha ta biyu wajen hadahadar kasuwanci a Najeriya, kuma wadda tafi kowane jiha karfin kasuwanci a arewacin kasar, jihar Kano nada kamfanunuwan sarrafa fata, na hada takalma, masaku, kamfanin hada magunguna da sauran kamfanunuwa da suka hada dana sarrafa kayan amfanin noma daban daban. duk da cewa a shekarun 2011-2013 jihar bata samu kudaden shiga ba da yawa, amma duk da haka har yanzu Kano itace cibiyar fitar da amfanin noma zuwa kasashen waje, kamar su; fata, auduga, gyada da sauransu.
Jihar Oyo itace jiha ta 5 a yawan mutane a Najeriya, kuma yawan filayen noman ta zasu iya riketa a wannan lokacin na karyewar tattalin arziki. Sai dai haryanzu ma’aikatan jihar na bin gwamnatin jihar bashin albashi, amma yawancin ma’aikatan jihar su fantsama harkar noma.
Tun kafin a gano mai a jihar Ribas, noma shi ne muhimmin sana’ar al’ummar jihar, sakamakon noman doya, rogo, makani, masara, shinkafa da wake daya yawaita a jihar. Sa’annan ana noman kwakwan manja, kwakwa, ayaba, agushi, attarugu, mangwaro da roba duk a jihar. Sa’annan jama’an jihar sun baiwa harkar kamun kifi wato Su muhimmanci sosai.
Duk da cewa karyewar farashin man fetur ya sanya jihohi da dama neman sabbin hanyoyin samun kudaden shiga, amma har yanzu jihohi kalilan ne suka cimma wannan manufa. Sai dai ita kanta gwamnatin tarayya ta kasa sauya hanyar samun kudaden shiga sakamakon yawan dogaro da tayi akan man fetur.
Asali: Legit.ng