Hakeem Baba Ahmed Ya Fadi abin da Ya Sani kan Alakar Tinubu da Shettima a Villa
- Hakeem Baba-Ahmed ya ce bai taba gudanar da aikin mai ba shugaban kasa shawara ba duk da watannin da ya shafe a ofis
- Ya bayyana cewa bai ji kwarin gwiwar cewa gwamnatin tarayya na da niyyar gyara kasa ba, dalilin da ya sa ya ajiye aikinsa
- Tsohon kakakin na ACF ya kara da cewa babu wata baraka tsakanin shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun kungiyar Arewa ta ACF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce bai taba gudanar da wani aiki ba a matsayin mai ba shugaban kasa shawara.
Baya ga haka, Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana abubuwan da ya gani dangane da alakar Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV cikin shirin Politics Today a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2023 ne aka nada shi a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, kafin ya ajiye mukamin a watan Afrilu.
Hakeem Baba Ahmed bai yi aiki a Aso Villa ba
Hakeem Baba-Ahmed ya ce duk da mukamin da aka ba shi, bai gudanar da wani aiki na ba da shawara ba:
“A’a, ban yi wani aiki ba. Ya kamata a ce ni mai ba shugaban kasa shawara ne, amma ban taba ba shi shawara ba,”
Ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi ganawa da shi a sirrance amma ya ki amincewa da hakan.
Da aka tambaye shi ko ya yi nadama kan shiga gwamnatin Bola Tinubu, Baba-Ahmed ya ce:
“Ban yi nadama ba, amma na bar aikin ne saboda ban ga irin jajircewar da ake bukata wajen gyaran kasa ba.”
Ya kara da cewa ya yi murabus ne domin bai ga wani yunƙuri daga gwamnati wajen cika alkawuran da ta dauka na sauya rayuwar ‘yan Najeriya ba,
Dr. Hakeem Baba ya ce babu wani muhimmin kokari da aka yi wajen yakar talauci da rashin tsaro a Arewacin kasar.
Batun sabani tsakanin Tinubu da Kashim Shettima
Game da rade-radin cewa akwai sabani tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa, Baba-Ahmed ya ce babu wata matsala a tsakaninsu.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
“A’a, ban ga wani alamar sabani a tsakaninsu ba. Alakarsu tana da kyau.”
Ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa Shettima kan yaba wa shugabancin Tinubu ko yaushe, yana cewa yana da kyakkyawar niyya ga kasar.

Source: Facebook
Sai dai Baba-Ahmed ya ce:
“A wasu lokuta na taba tambayarsa, idan da gaske shugaban kasa na da niyya mai kyau, me yasa abubuwa da dama ke tafiya ba daidai ba?”
Ya kammala da cewa bai da niyyar sake karbar wani mukami a karkashin gwamnatin Tinubu a nan gaba.
Ahmed Isa ya caccaki Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Ahmed Isah na Brekete Family ya caccaki tsare tsaren shugaba Bola Tinubu.
Ahmed Isah ya ce bai dace gwamnatin Bola Tinubu ta sanya wutar sola a fadar shugaban kasa ba alhali ana fama da wahalar rayuwa.
Ya bayyana cewa ya fi kamata gwamnatin tarayya ta yi amfani da kudin wajen samar da masana'antar da za a rika hada sola a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


