Shehu Sani Ya Lissafa Abubuwa 5 da Ke Lalata Albashin Ma’aikata a Najeriya
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana manyan abubuwa biyar da ke lalata albashin ma'aikata a Najeriya
- Shehu Sani ya yi nuni da cewa wadannan abubuwa da suka hada da hauhawar farashi da cire tallafi, na rage darajar albashin ma'aikata
- ‘Yan Najeriya sun mayar da martani mai zafi, wasu sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da kawo manufofin da ke jefa talaka cikin kunci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana abubuwa guda biyar da ke lalata albashin ma’aikata a Najeriya.
Sanata Shehu Sani ya ce wadannan abubuwa guda biyar suna rage darajar albashi, musamman ma na kananun ma’aikatan kasar.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (@ShehuSani) yayin bikin ranar ma’aikata a ranar Alhamis, 1 ga Mayu, 2025.
Abubuwa 5 da ke lalata albashin ma'aikata
Sanatan ya lissafa abubuwan kamar haka:
- Cire tallafi.
- Karin farashin wutar lantarki da na sadarwa.
- Tsadar farashin kayan masarufi (hauhawar farashi).
- Faduwar darajar Naira.
- Karin kudin haya.
'Yan Najeriya sun yi wa Shehu Sani martani
Wani mahaukacin gwamnati a Katsina, Abdulmumini Sani, ya ce maganar Sanya Shehu Sani gaskiya ce, domin dalilan da ya kawo su ne ke cinye albashi gaba daya.
"Tsadar kayan masarufi ya sa mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba zai wadatar da maaikaci ba, domin ko buhun shinkafa ba za ka iya siya ba.
"Idan ka lura, shinkafa, tuwo, kunu su ne dai yanzu aka fi ci, to ko wadannan, za su cinye N70,000 tas har da neman kari, kafin a zo maganar lafiya, sutura da sauransu."
Abdulmumini Sani ya ce janye tallafin man fetur ya sa zirga-zirga ta yi tsada, inda albashin maaikaci kan zama wofi saboda biyan kudin acaba ko tasi zuwa wajen aiki.
"Lallai dai ya kamata a sake duba mafi ƙarancin albashin nan kamar yadda NLC ta nema a ranar maaikata ta 2025. Ma'aikata na cikin mawuyacin hali."
- Abdulmumini Sani.
Legit Hausa ta kuma tattaro wasu daga cikin martanin 'yan Najeriya kan abubuwan da ke lalata albashi da Shehu Sani ya zayyano:
@yommix:
“Duk da cewa yana da kyau a san hakan, amma zai fi amfani idan ka shaida wa mutane cewa manufofin abokinka, Tinubu, su ne musabbabin lalacewar rayuwar mutane.”
@TankoZ3:
“Gaskiya ne. Wadannan dalilai da aka lissafa su ne ke jefa mu cikin wahala.”
@jgoldmonye:
“Ya kamata mafi karancin albashi a Najeriya yanzu ya zama ₦500,000. APC ta lalata Najeriya da siyasar danniya. Tinubu yana tara komai wa kansa da mukarrabansa. Duk wanda ya yi masa hidima daga Yarbawa, sai a jefa bude masa kofar tara kudi.”

Source: Facebook
Wasu mabiyan tsohon sanatan sun kara da cewa:
@shortstories_s:
“Kai gaskiya ka fada. A bayyane yake cewa wannan gwamnati ba ta da tausayi. Yaya mutum zai cire tallafi, ya karya darajar Naira, ya kara kudin wuta da sadarwa duka lokaci daya? Wadannan manufofi sun munana, kuma akwai masifa a tare da su."
@Aminusaid_:
“Kuma har yanzu sun ki daukar matakan gyara. Ban san ko akwai wani tsammanin kyakkyawar rayuwa da ya rage wa ‘yan Najeriya ba.”
@CameronWaigha:
“Amma ka san hauhawar farashi matsala ce tun da dadewa. Da NLC ta hada kai da masana tattalin arziki don taimaka masu wajen tattaunawa, da ba a shiga wannan hali ba. Idan albashi na bin CPI, da komai ya tafi da sauki, ko ba haka ba?”
Gwamnan Edo ya karawa ma'aikata albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Monday Okpebholo ya amince da sabon mafi karancin albashi na ₦75,000 ga ma’aikatan Edo domin inganta rayuwarsu.
Ya bayyana cewa gwamnati ta mayar da ma’aikatan wucin-gadi zuwa cikakkun ma’aikata tare da ɗaukar sabbin malamai da ma’aikatan lafiya.
Gwamna Okpebholo ya jinjinawa kokarin ma’aikatan jihar Edo, inda ya ce gwamnatin sa na aiki tukuru don magance matsalolin da suke fuskanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


