Ana Wata ga Wata: ICPC Ta Bankado Rashawar Naira Biliyan 71.2 a Gwamnatin Tinubu
- Hukumar ICPC ta ce daga cikin Naira biliyan 100 da aka ware, biliyan 28.8 ne kacal suka kai hannun dalibai a karkashin shirin ba da rancen karatu
- ICPC ta ce an gayyaci shugabannin NELFUND da jami’an gwamnati don su yi mata bayani kan Naira biliyan 71.2 da suka yi batan dabo daga shirin
- Yayin da ICPC ta yi bayanin yadda NELFUND ya samu Naira biliyan 100, hukumar ta sha alwashin gano wadanda suka wawure Naira biliyan 71.2
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta kaddamar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen rashin gaskiya a yadda ake raba bashin dalibai ta asusun NELFUND.
ICPC ta Naira biliyan 28.8 ne kacal suka isa hannun dalibai a jami'o'i da manyan makarantu daga cikin Naira biliyan 100 da aka wayar domin bayar da rancen karatun.

Source: Facebook
Ana zargin makarantu da zabtare bashin dalibai
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ICPC, Demola Bakare, ya fitar a ranar Alhamis, 1 ga Mayu, 2025, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken hukumar ya faro ne daga rahotannin kafafen watsa labarai da suka zargi makarantu 51 da wawure kudaden dalibai tare da zama masu cin gajiyar shirin NELFUND.
Rahotannin sun bayyana cewa makarantun na cire kudade daga N3,500 zuwa N30,000 daga kudaden makarantar dalibai da aka biya karkashin bashin karatun.
ICPC ta fara bincike kan badakalar N71.2bn
Binciken farko ya gano babban gibi a cikin tsarin rabon kudaden, inda aka nemi Naira biliyan 71.2 sama ko kasa aka rasa, lamarin da ya sa ICPC ta soma gudanar da bincike nan take.
Sanarwar ta shaida cewa:
“An aika da takardun bincike da gayyata zuwa ga manyan jami’an gwamnati da suka hada da darakta janar na ofishin kasafin kudi, akanta janar na tarayya, da kuma manyan jami’ai daga babban bankin Najeriya (CBN)."
Hakazalika, ICPC ta gayyaci shugaban hukuma da darakta janar na asusun NELFUND domin gabatar da takardu da bayanai kan batan kudaden, inji rahoton Punch.
Zargin batan biliyoyi daga asusun NELFUND
Demola Bakare ya kara da cewa:
“Ya zuwa yanzu an tantance amsoshin da aka samu, sannan an gudanar da tattaunawa da wadanda lamarin ya shafa.”
Sakamakon binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawar ya nuna cewa har zuwa ranar 19 ga Maris, 2024, NELFUND ta karɓi jimillar Naira biliyan 203.8.
“Shige da ficen kudaden ya nuna cewa Naira biliyan 10 sun fito daga asusun raba kudin tarayya (FAAC), Naira biliyan 50 daga hukumar EFCC, sai kuma Naira biliyan 71.9 da wata Naira biliyan 71.9 suka fito daga TETFund a lokuta daban daban."

Source: Facebook
ICPC za ta gano badakala a shirin NELFUND
Duk da wannan dimbin kudi, rahotanni sun nuna cewa Naira biliyan 44.2 kacal aka rabawa makarantu tun lokacin da aka kafa asusun.
“Zuwa yanzu, jimillar kudin da aka rabawa makarantu 299 masu cin gajiyar shirin ya kai kusan Naira biliyan 44.2, inda dalibai 293,178 suka ci gajiyar shirin,” inji ICPC.
ICPC ta tabbatar da cewa an gano wasu kura-kurai a tafiyar da shirin rancen karatun, kuma yanzu haka an fadada binciken zuwa ga makarantun da suka ci gajiyar shirin da kuma daliban da suka karɓi bashin.
ICPC za ta kwato N1bn da aka karkatar a Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ta ba da umarnin kwato Naira biliyan 1.37 da ake zargin an karkatar daga baitul malin jihar Kaduna zuwa wani asusun sirri.
Kudin na daga cikin wadanda aka ware don aikin jirgin kasa na zamani wanda bai tabbata ba a lokacin mulkin tsohon gwamna Mallam Nasir El-Rufai.
Mai shari’a H. Buhari ne ya bayar da umarnin kwace kudin na wucin gadi a ranar 28 ga Fabrairu, bayan bukatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shigar a kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


