Gwamna Ya Sake Karawa Ma'aikata Albashi, Zai Dawo Biyan N75,000 maimakon N70,000
- Gwamna Monday Okpebholo ya amince da sabon mafi karancin albashi na ₦75,000 ga ma’aikatan jihar Edo don inganta rayuwarsu
- Ya ce gwamnatin sa ta mayar da daruruwan ma’aikatan wucin-gadi zuwa cikakkun ma’aikata, tare da ɗaukar sabbin malamai da ma’aikatan lafiya
- Gwamnan ya yaba da jajircewar ma’aikata a fannoni daban-daban, ya kuma ce gwamnati na kokarin magance ƙalubalen da suke fuskanta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Gwamna Monday Okpebholo ya sanar da ƙarin mafi karancin albashi daga ₦70,000 zuwa ₦75,000 ga ma’aikatan jihar Edo don inganta rayuwarsu.
Ya bayyana karin albashin ne a ranar Alhamis, yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke Birnin Benin.

Source: Twitter
Gwamna ya kara wa ma'aikatan Edo albashi
A cewar rahoton Punch, Gwamna Okpebholo ya shaida wa ma'aikatan Edo cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Cike da farin ciki a yau, muke sanar da cewa mun amince da sabon mafi ƙarancin albashi na ₦75,000 ga ma’aikatan Edo."
Ya ce wannan ƙari wata hanya ce ta nuna godiya ga ma’aikatan jihar, tare da fatan za su ƙara himma wajen ganin Edo ta ci gaba.
Gwamnan ya kara da cewa daga lokacin da ya hau mulki, gwamnatinsa ta ba da fifiko mai girma ga walwalar ma’aikata a jihar.
Gwamnatin Edo ta dauki sababbin ma'aikata
Ya ce daga cikin abubuwan farko da suka yi akwai mayar da dubban ma’aikatan wucin gadi, ciki har da masu shara 1,000, zuwa cikakkun ma’aikatan gwamnati.
Gwamna Okpebholo ya kuma ce sun ɗauki malamai 500 aiki don rage cunkoson dalibai a aji da inganta harkar koyo da koyarwa a fadin jihar.
Haka kuma, ya ce gwamnati na duba yiwuwar mayar da fiye da malamai 3,000 da ke matsayin ma’aikatan wucin-gadi zuwa cikakkun ma’aikata.
“Mun amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya 450, ciki har da masu aikin likitanci da wadanda ba likitoci ba, don ƙarfafa ayyuka a asibitocinmu,” inji gwamnan.
Gwamnan Edo ya jinjinawa ma'aikatan jihar
Ya ce gwamnati ta kuma daidaita matsayin ma’aikatan kwangila 126 a asibitin kwararru na jihar Edo domin tabbatar da kwanciyar hankalinsu da kara masu kaimi a aiki.
Tun da fari, gwamnan ya mika sakon gaisuwa ga ma’aikata na jihar da na duniya baki ɗaya yayin da ake bikin ranar ma’aikata ta duniya, inji rahoton Channels TV.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Fred Itua ya fitar, ya yabawa jajircewa da gagarumar gudunmawar ma’aikata a ci gaban jihar.
Sanarwar ta ce ma’aikata ne ginshiƙai na tattalin arziki da ci gaban al’umma, kuma kokarinsu yana tasiri kai tsaye kan makomar Edo.
Gwamnan Edo zai magance matsalolin ma'aikata
Gwamnan ya yaba da jajircewar ma’aikatan da ke aiki a fannoni daban-daban kamar kiwon lafiya, ilimi, sana’o’i da harkokin kasuwanci.
Sanarwar ta ce bikin ranar ma’aikata na bana dama ce ta nuna godiya ga ma’aikatan Edo da tabbatar da goyon bayan gwamnati gare su.
Gwamna Okpebholo ya ce yana sane da ƙalubalen da ma’aikata ke fuskanta, kuma ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kokari wajen magance su.
Gwamnan Edo ya amince da sabon albashin N70,000
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Edo ta fara aiwatar da biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga duk ma’aikatan gwamnati a fadin jihar.
Gwamna Godwin Obaseki ne ya dauki wannan mataki bayan da ya sha alwashin kara albashin ma’aikatan jihar domin inganta rayuwarsu.
An fara biyan sabon albashin ne tun daga watan Mayu 2024, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar da cika alkawarin da ta daukarwa ma'aikatan.
Asali: Legit.ng


