A karshe, Ahmad Isa na Brekete Family Ya Yi Magana, Ya Caccaki Tinubu

A karshe, Ahmad Isa na Brekete Family Ya Yi Magana, Ya Caccaki Tinubu

  • Ahmad Isa na Brekete Family ya bayyana cewa yana raye kuma ba a kama shi ba kamar yadda ake yadawa kwanan nan
  • Baya ga haka, ya bukaci ‘yan Najeriya su zauna lafiya tare da ci gaba da kaunar ƙasar su duk da halin da ake ciki
  • Ya soki gwamnatin tarayya kan shirin kashe N10bn don samar da wutar sola a Fadar Villa, ya ce hakan rashin fifita talaka ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai gabatar da shirin Brekete Family, Ahmad Isa wanda aka fi sani da “Ordinary President”, ya fito ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa ko dai ya mutu ko kuma an kama shi.

Ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya yi a ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, domin warware rudani da damuwar da ta shiga zukatan masoyansa.

Kara karanta wannan

A karshe, ISWAP ta dauki alhakin dasa bam da ya kashe mutane 26 a Borno

Brekete Family
Ahmad Isa ya karyata jita jitar kama shi. Hoto: Brekete Family.
Source: Facebook

Legit ta rahoto cewa tashar Brekete Family ta wallafa maganar da Ahmed Isa ya yi a shafinta na YouTube.

A cikin jawabinsa, Ahmad Isa ya ce yana nan da rai kuma yana cikin koshin lafiya, yana mai cewa:

“Wasu na cewa na mutu, wasu na cewa an kama ni. Amma kamar yadda kuke ji da kunnenku, ba a tsare ni ba kuma ban mutu ba.”

Ya ce ya yanke shawarar magana ne saboda yawan kira da sakonnin da ya rika samu daga mutane da ke damuwa da inda yake.

“Ko na mutu, wasu za su cigaba” — Ahmad Isa

Ahmad Isa ya kara da cewa ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, domin ko da ya mutu wasu za su ci gaba daga inda ya tsaya.

Ya bukaci mutane su ci gaba da nuna ƙaunar ƙasarsu, su daina fushi da Najeriya saboda matsalolin da ake fuskanta a yanzu.

Kara karanta wannan

Dele Momodu ya fito da bayani kan rade radin komawar Atiku APC

Ya ce:

“Zan ci gaba da magana har sai Najeriya ta gyaru, domin wannan ƙasa tamu ce, ba mu da wata da za mu koma.”

Ahmed Isa ya soki shirin saka sola a Aso Villa

A cikin jawabin nasa, Ordinary President ya bayyana rashin jin daɗinsa kan wani shiri na gwamnatin Bola Tinubu na kashe Naira biliyan 10 wajen saka sola a Villa.

Ya ce wannan lamari ba shi da alfanu ga talakawa, kuma kamata ya yi a mayar da hankali kan gyaran rayuwar ‘yan kasa.

A cewar shi:

“Da za a yi amfani da kudin nan wajen kafa masana’antar sola, da tuni an samar da ayyuka ga daruruwan matasa,”
Tinubu
Ahmad Isa ya bukaci Tinubu ya mayar da hankali kan bukatun talaka. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga Bola Tinubu ya yi taka tsan-tsan da 'yan siyasa masu sauya sheka zuwa APC domin cimma bukatun kansu.

Ahmed Isa ya yaba da farkawar 'yan Arewa

Ahmad Isa ya kuma bayyana jin daɗinsa da yadda matasan Arewacin Najeriya suka fara farkawa domin tunkarar lamura da gaske.

Kara karanta wannan

'Dole Tinubu ya zarce,' Minista ya bukaci 'yan APC su tashi tsaye kan 2027

Ya sha alwashin ci gaba da kalubalantar yadda ake tafiyar da lamuran tsaro a Arewa har sai an samu gyara.

Ordinary President ya yi zargin cewa an ga 'yan Arewa sun fara hada kai ne shi yasa aka fara kai hare hare kauyuka domin raba kansu.

Legit ta tattauna da Adamu Saidu

Wani mai bibiyan Brekete Family, Adamu Saidu ya bayyana wa Legit cewa ya yi farin ciki da ya ji labarin Ahmad Isa yana lafiya.

Adamu Saidu ya ce:

"Dole mutane su damu ganin yadda ya dauko aikin wayar da kan al'umma. Amma yanzu hankalin mu ya kwanta yanzu.
"Muna masa addu'a Allah ya cigaba da kare shi, ya kawo mana sauki a Najeriya."

An kai hari kan masu zaman makoki a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan ta'adda da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari ajihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa na kai harin ne a lokacin da wasu mutane suke zaman makoki a yankin Chibok.

Legit ta rahoto cewa maharan sun kashe mutane kimanin 15, aka jikkata da dama tare da kona gidaje da coci yayin harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng