2027: Daliban Arewa daga Jihohi 19 Sun Gana da Atiku Abubakar a Abuja

2027: Daliban Arewa daga Jihohi 19 Sun Gana da Atiku Abubakar a Abuja

  • Kungiyoyin dalibai daga jihohin Arewa 19 sun gana da Atiku Abubakar a ranar Laraba domin tattauna batutuwan kasa da ilimi
  • Matasan sun yabawa tsohon mataimakin shugaban kasar bisa jajircewarsa wajen ciyar da Najeriya da kuma manyan gobe gaba
  • Wazirin Adamawa ya ba su tabbacin hada kai da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa don samar da nagartaccen shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karɓi bakuncin kungiyoyin dalibai daga jihohin Arewa 19 da kuma kungiyar daliban Jihar Kano.

Ganawar Atiku Abubakar da daliban ta mayar da hankali kan halin da Najeriya ke ciki da kuma sha’anin ilimi.

Atiku
Kungiyar daliban Arewa ta ziyarci Atiku. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda ganawar ta gudana ne a cikin wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Giwa: Gobara ta tashi a rumbun makaman sojojin Najeriya a Maiduguri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban gamayyar daliban jihohin Arewa, Kwamared Sani Danmasani da shugaban kungiyar daliban Jihar Kano, Ishaku Ali Kanwa, ne suka jagoranci tawagar.

Sun bayyana farin cikinsu da irin goyon bayan da Atiku ke bai wa fannin ilimi da ci gaban matasa.

Atiku ya yaba da kokarin daliban Arewa

Atiku ya bayyana farin cikinsa da irin fatan cigaba da daliban suka nuna, yana mai karfafa musu gwiwa kada su yi kasa a gwiwa wajen neman canji a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

"Na yi farin ciki da yadda suke nuna kwazo da kishin kasa. Na tabbatar musu cewa zan hada karfi da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa don samar da shugabanci nagari da zai tabbatar da makoma mafi kyau ga ‘yan kasa."

Ya kuma yi kira ga matasa da su ci gaba da zama masu himma da kishin kasa domin dorewar cigaba a Najeriya, musamman a fannin ilimi da ke da matukar tasiri wajen gina kasa.

Kara karanta wannan

Dangote ya samu babban mukami a bankin duniya, Tinubu ya taya shi murna

Atiku
Atiku ya ce zai cigaba da tallafawa ilimi. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Depositphotos

Martanin mai goyon bayan Atiku kan ziyarar

Daya daga cikin magoya bayan Atiku, Kabiru Abdulazeez, ya yaba da yadda aka yi taron tare da mika bukatar dawo da tsarin karatun firamare da sakandare kyauta ga matasa.

Ya bayyana cewa tsarin makarantar da ya kammala karatu a ciki a shekarun 1980 zai zama ginshiki ko misali wajen sake fasalin tsarin ilimi a kasar nan.

Kabiru ya bayyana yadda yake burin ganin tsarin karatu ya kasance idan Allah ya ba Atiku nasara a 2027:

“A tabbatar da cewa aji bai wuce ɗalibai 20 ba, tare da samar da ina gine-gine, malamai da kayan aikin da suka dace,”

Ya ce burinsu shi ne ganin an mayar da Najeriya kasa mai gaskiya da rikon amana, tare da mayar da ilimi abin alfahari ga kowane dan kasa.

Momodu: 'Atiku ba zai koma APC ba'

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar ba zai koma APC ba.

Kara karanta wannan

Bayan bindige shanu 37 a Filato, Amurka ta shiga harkar makiyaya a Najeriya

Dele Momodu ya ce maganar da ake yi ta cewa Atiku Abubakar zai koma APC bata da tushe balle makama.

Baya ga haka, Momodu ya ce sauya sheka da 'yan PDP suka yi a Delta ya nuna yadda aka rasa masu akida a siyasar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng