Sarki Muhammadu Sanusi II zai Gudanar da Hawan Babban Daki a Kano
- Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zai gudanar da Hawan Babban Daki a yau Asabar bayan dawowarsa daga birnin London
- Masu sharhi da magoya baya sun yi addu’o’in fatan alheri ga Sarki Sanusi II domin Allah ya sa a yi taron lafiya ba tare da tashin hankali ba
- A gefe guda kuma, Sarki Aminu Ado Bayero ya halarci wani taro tare da wasu sarakunan Arewa a Kaduna bayan dawowa daga Umrah
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Fadar Masarautar Kano ta sanar cewa mai martaba, Khalifa Muhammad Sanusi II, zai gudanar da Hawan Babban Daki a yau Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da hawan ne da misalin karfe 4:00 na yamma, bayan dawowarsa daga London.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanan da masarautar Kano ta fitar ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masarautar ta sanar da cewa:
"Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, CON zai gudanar da Hawan Babban Daki yau Asabar da Misalin Karfe 4:00 Na Yamma Insha Allah.
Mutane sun yi wa Sanusi II fatan alheri
Mutane da dama sun nuna farin cikinsu da kuma yi wa Sarki Sanusi II fatan alheri da nasara a kan wannan hawan.
Nafiu Sabo Gumel ya bayyana cewa:
"Masha Allah, Allah ya kara wa Khalipha lafiya, a yi hawa lafiya a sauko lafiya, ya kara wa mai babban daki lafiya, ameen."
Haka zalika, Usman Sambo ya yi magana yana nuna girmamawarsa da farin cikinsa da dawowar sarkin:
"Baban wanka. Ga kudi, ga ilmi, ga sarauta,"
Kabir Ahmed kuwa ya yi addu'a domin samun zaman lafiya da dorewar a jihar Kano, inda ya ce:
"Allah ya ba mai babban daki lafiya da tsawon rai,"
Shirye-shiryen taron hawan babban daki
A cewar rahotanni, ana sa ran cewa Sarki Sanusi II zai gudanar da hawan ne a kan rakumi, wanda al’ada ce da ke nuna kima da martabar hawan.
Mutane da dama daga sassa daban-daban na jihar da ma waje suna shirin halartar wannan hawan domin tarbar Sarkin da kuma nuna biyayya ga masarauta.
Sarki Aminu Ado Bayero na taro a Kaduna
A daya bangaren kuwa, Mai Martaba Sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya halarci wani taro a jihar Kaduna tare da wasu manyan sarakuna.

Source: Facebook
A cewar wata sanarwa, Sarkin ya hadu da Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Mohammed Sani II da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq a taron da aka gudanar yau Asabar a Kaduna.
Masarautar Kano ta tabbatar da taron da mai martaba Aminu Ado ya halarta a Kaduna a wani sako da ta wallafa a X.
Aminu Ado ya yaba wa Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Aminu Ado Bayero ya yabawa shugaba Bola Ahmed Tinbu kan ayyukan da yake yi.
Sarkin ya bayyana cewa shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje na taka muhimmiyar rawa wajen kawo cigaba.
Mai martaba Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa dama duk inda aka samu Ganduje akwai alamar za a yi aiki yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


