An Kama Mahaifi da Kishiya bayan Jawo Guntule Kafafun Dansu a Kaduna

An Kama Mahaifi da Kishiya bayan Jawo Guntule Kafafun Dansu a Kaduna

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta ceto wani yaro mai shekara 7 da mahaifinsa ya azabtar, lamarin da ya kai ga yanke masa ƙafafu biyu
  • Mahaifin yaron ya daure masa ƙafa sannan ya zuba masa ruwan zafi saboda zargin satar biskit, lamarin da ya kai ga raunin yanke ƙafafun
  • An cafke mahaifin da kishiyar mahaifiyar yaron, kuma gwamnati ta sha alwashin gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - An ci zarafin wani yaro a karamar hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, inda wani uba da matarsa suka yi wa ɗansa duka da azabtarwa har ya rasa ƙafafunsa.

An ce mahaifin yaron mai suna Sani Tanimi ne ya aikata danyen aikin, bayan da ya zarge shi da satar biskit.

Kara karanta wannan

Yadda aka kuskure Natasha wajen kai hari gidansu da agajin da 'yan gari suka kai

Kaduna
An kama mahaifi da kishiya kan zargin cin zarafin yaro. Hoto: Inside Kaduna
Source: Facebook

Rahoton jaridar the Guardian ya tabbatar da cewa an kwantar da yaron mai suna Abubakar Sani a asibiti.

Lamari ya tayar da hankula, inda hukumar kula da walwalar jama’a da ci gaban al’umma ta jihar Kaduna ta ce za ta ɗauki matakin shari’a a kan wadanda ake zargin.

Dalilin da ya sa aka guntule kafafun yaro

An ruwaito cewa mahaifin yaron ya daure shi sannan ya zuba masa ruwan zafi a ƙafafunsa, lamarin da ya janyo munanan raunuka da suka yi muni har sai da aka yanke ƙafafunsa.

Likitoci a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko sun bayyana cewa dole ne a yanke ƙafafun daga ƙasa da gwiwa domin ceto rayuwar yaron.

Kwamishinar jin ƙai da ci gaban al’umma, Hajiya Halima Salisu, ta kai ziyara asibitin don duba lafiyar yaron, inda ta ce lamarin ya girgiza su matuƙa.

An cafke uban yaron da kishiyar mamarsa

Kara karanta wannan

Rana ta baci: Mota ta banke barawo lokacin da ya saci babur a masallaci

Kwamishinar ta tabbatar da cewa an kama mahaifin yaron da kishiyar mamarsa, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Rahoton Trust TV ya nuna cewa Halima Salisu ta ce an kulle yaron fiye da kwana 20 ba tare da abinci mai kyau ba, kuma hakan ya ci karo da dokar kariyar yara da jihar ta kafa.

Ta bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci cin zarafin yara, fyade ko tashin hankali ba, tana mai kira ga jama’a da su rika sanar da rahoton irin wannan danyen aikin.

Uba Sani
Gwamnatin Kaduna za ta dauki mataki kan iyayen da ake zargi da yi wa dansu rauni. Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Za a sanya wa yaron kafafun roba

Shugaban asibitin Barau Dikko, Dr Abdulkadir Musa, ya ce ko da yake an yanke ƙafafun, akwai yiwuwar a sanya masa ƙafafu na roba a gaba.

Ya bukaci iyaye da su rika yin haƙuri da juriya wajen gyara tarbiyyar yara, domin yin hukuncin da ya wuce gona da iri ne ke haifar da barnar da ba za a iya gyarawa ba.

An saka wa shanu guba a Filato

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta hukunta matashin da ya yi yunkurin cakawa mahaifinsa makami

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Filato ta fara bincike kan wasu shanu da ake zargin an saka wa guba a abinci.

Dakarun soji sun isa wajen da lamarin ya faru a karamar hukumar Bassa domin hana daukar fansa da tabbatar da zaman lafiya.

Legit ta rahoto cewa shanu sama da 30 ne aka sanya wa guba a ganyen kayan lambu, amma likitocin dabbobi suna bincike domin tattabar da gaskiyar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng