Da kaina na yi ta son a yanke kafata domin na huta – Sani Moda
Shahararren dan wasan nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Sani Moda ya ce bai kamata mutane su rinka nuna damuwarsu ba domin Allah ya sauya musu halitta.
A hira da yayi da shafin BBC Hausa, jarumin ya bayyana cewa ya kasance da kansa yake rokon likita da ya yanke masa kafarsa saboda irin azabar ciwon da ta yi masa.
Ga cikakken jawabinsa: "A ranar da ya ce min za a cire wannan kafar, ji nake kamar an ba ni bisar Makkah. A wannan lokaci ana wanke mun kafa da hannuna nake cire jijiyoyin kafar da suka mutu, ina tince su haka ina zubarwa.
"Idan na daga kafar ina so na yi tafiya ba na ma iya tafiya tunda daukata ake yi kamar jariri.
"A wannan lokaci na ji dadi da farin cikin cewa za a cire kafar. Amma na ce wace rana? Ranar Talata muka yi Magana dashi, ya ce jibi idan Allah ya kaimu Alhamis za a yi aiki a kafar.
"To wallahi sai gani nake kamar ranar Alhamis din ba za ta yi ba. Saboda ina so nayi bacci sai na daga kafafuna, toh komin dare fa idan na farka sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
"A wannan ranar Alhamis na yi bacci na manta da asubahi ranar Juma’a cewa an cire mun kafa. Da na tashi zan mike akan gadon asibitin sai na fara sauka da kafar da aka yanke, sai na fadi. Sai na sa kafafuna guda biyu na daga hannu nayi godiya ga Allah, yau ya kai ga jiya zuwa watannin da suka gabata an kai lokacin da bana iya bacci, gashi yanzu an cire har na manta da laluran da nake ciki. Saboda haka rayuwata babu wani abunda ya sauya tunda dai bai hana ni ci ko sha ba.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini a wata jihar arewa, sun bukaci iyalansa su fara tara kudin fansa
"Da babu Sani Moda, Allah ya samar da shi. Ya raine ni har zuwa shekara 50 da wani abu, ya wadata ni da gidan da nake ciki, ya ba ni iyali, ya daukaka ni daga cikin al’umma ta sannaya wanda za a iya cewa ga wane. Toh yau kuma ga yadda ya mayar da Sani. Toh wajen wa zan kai wannan gaba?"
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng