An Yanke Wa Wata Ɗaliba Ƙafa A Ranar Da Suka Kammala Makaranta A Sokoto

An Yanke Wa Wata Ɗaliba Ƙafa A Ranar Da Suka Kammala Makaranta A Sokoto

  • Kaddara ya fada kan wata daliba Fatima Suleiman yar makarantar Khalifa International School a ranar da suka kammala jarrabawar karshe
  • Fatima suna tsaye tare da kawayenta ne suka jiran iyayensu su zo daukansu a yayin da wani dalibi ya taho a afka musu da mota, ya yi mata mummunan rauni a kafa
  • Bayan an garzaya da Fatima asibiti, likitoci suka bada shawarar a yanke kafar daya saboda munin raunin, a halin yanzu tana rokon a tallafa mata da kafan roba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Wata daliba mace yar makarantar Khalifa International Model School, Fatima Suleiman, wacce ta rasa kafarta daya a lokacin da wani dalibi ya buge ta da mota a ranar da suka kammala makaranta, tana neman kafa na roba.

Taswirar JIhar Sokoto.
An Yanke Wa Wata Ɗaliba Ƙafa A Ranar Da Suka Kammala Makaranta A Sokoto. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: UGC

Yadda abin ya faru

An tattaro cewa Fatima da kawayenta suna jiran iyayensu su zo su dauke su daga makaranta ne a ranar yayin da wani dalibi ya afka musu da mota, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da cewa kawayenta sun tsira, Fatima ta samu munanan rauni.

Shugaban makarantar, Mr James, ya ce hukumar makarantar ta garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Danfodio tare da yan sanda, inda likitoci suka bada shawarar yanke kafarta saboda munin raunin.

Fatima na neman tallafin kafar roba

Ya ce bayan an yanke kafar, iyayen yarinyar suna neman tallafin kafa na roba domin taimakawa yarsu ta rika zirga-zirga kamar yadda ya zo a rahoton.

James ya kara da cewa hukumar makarantar sun rika taimakawa wacce abin ya faru da ita, wanda har yanzu tana asibiti, don ganin ta samu sauki cikin gaggawa.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel