'Duk Wanda Ya Bar Musulunci a Kashe Shi?': Dr Jalo Jalingo Ya Kare Hadisin Annabi
- Dr. Ibrahim Jalingo ya kare hukuncin kisa ga wanda yayi ridda, inda ya ce masu kalubalantar Hadisin Manzon Allah (SAW) jahilai ne
- Malamin addinin ya bayyana cewa Hadisi wahayi ne kamar Alkur’ani, wanda ya ke fassara nassoshin da Kur’ani ya kawo su a dunkule
- Ya ce Hadisin da ya ce a kashe wanda ya bar Musulunci bai saba da Kur’ani ba, tare da kiran Musussuka da 'jahili' kuma 'murakkabi'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Malamin addinin Musulunci kuma shugaba a majalisar malamai ta kasa a Izala, Dr. Ibrahim Jalingo, ya kare hukuncin kisa ga wadanda suka bar Musulunci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Dr. Jalingo ya kare Hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ce a kashe wanda ya yi ridda, tare da cewa masu sukar hadisin jahilai ne 'murakkab'.

Asali: Facebook
Malamin, a sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya fadi hakan ne a matsayin martani ga masu kalubalantar ingancin Hadisin, suna ikirarin cewa ya sabawa Alkur’ani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masussuka ya kalubalanci Hadisin Annabi
Dr Jalo Jalingo na martani ne ga wani Masussuka, wanda ya kira da 'shugaban 'yan kala kato a Najeriya, da aka ba kwangilar karyata hadisan Manzon Allah (SAW).
Masussuka, a cikin wani bidiyo da ya fitar, ya yi ikirarin cewa akwai hadisai guda 100 da suka saɓawa Al-ƙur'ani, kuma Musulmi masu imani da hadisai da Al-ƙur'ani ba za su iya kare su ba.
Hadisin farko da shi Masussuka ya kawo, shi ne hadisin da aka ruwaito Annabi yana cewa "duk wanda ya musanya addininsa, to ku kashe shi".
A cewar Masussuka, wannan hadisin ba shi da wata madogara a cikin Al-Kur'ani, kuma malamai ko masu bin hadisi ba za su iya kare wannan ikirari ba.
Jalo Jalingo ya magantu kan wahayin Hadisi
To sai dai a martanin da Dr. Jalingo ya yi wa Masussuka, ya ce:
"Ya kamata dukkan duniya ta san cewa babu inda Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: 'aikin Hadithi shi ne fassara Alkur’ani'. Amma Annnabi ya ce: 'Tabbas an ba ni Alkur’ani da kwatankwacinsa tare da shi'.
"Abin da yake hakika shi ne: Alkur’ani wahayi ne daga Allah, shi ma Hadithi wahayi ne daga Allah. Sau da dama Alkur’ani zai yi magana a kan mas’ala a dunkule ko a takaice, sannan wahayin Hadithi ya zo ya fadada magana a kan mas’alar.
Dr. Jalingo ya kare Hadisin Annabi

Asali: Facebook
Game da Hadisin da Masussuka ya ke magana a kansa, Dr. Jalingo ya ce:
"Wahayin Hadithi da (Masussuka) ka kawo inda Annabi ya ce: 'Duk wanda ya musunya addininsa ku kashe shi,' gaskiya ne kuma bai saba wa wahayin Alkur’ani ba; domin Allah ya ce a cikin Taubah, aya ta 5, 'Idan watanni masu alhurma suka wuce toh ku kashe mushrukai a duk inda kuka same su'.
"Kuma ya ce a cikin Bakara, aya ta 193, 'Ku yake su har sai in ya kasance babu wata fitina, kuma Addini ya zamanto na Allah ne kadai.' Ma’ana ku yake su har sai sun Musulunta.
"Kuma ya ce a cikin Nisa’i, aya ta 89, 'Ku kashe su a duk inda kuka same su'. Ya kuma sake cewa a cikin Nisa’i, aya ta 91, 'Ku kashe su a duk inda kuka tarar da su.'
"Kun ga in ba jahili ba irin Masussuka babu wanda zai ce wahayin Hadithi da ya ce: 'Wanda ya musanya addininsa ku kashe shi' ya saba wa Alkur’ani; domin shi ma Alkur’anin abin da ya ce ke nan har ma da kari; domin shi Alkur’ani ba ma wanda ya yi ridda ba kadai ya ce a kashe, a’a dukkan Mushrukai ne ya halatta a kashe su."
Dr. Ibrahim Jalingo ya ce wannan shi ne takaitaccen raddi ga "wannan jahilci murakkabi mai fiska irin ta karuwai da yan daudu", watau Masussuka.
Dr Jalingo ya sha rubdugu kan 'Qur'anic Festival'
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, ya magantu game da shirin bikin Qur'anic Festival da aka so gudanarwa a Fabrairu.
Wasu matasa a kafafen sada zumunta sun yi suka kan hujjojin Dr. Jalingo, suna masu cewa irin wannan taro bai dace da ka’idojin koyarwar Sunnah ba.
Sai dai wasu daga cikin mabiya Izala sun bayyana cewa suna kan tafarkin Sunnah, kuma babban manufar wannan taro ita ce yada ilimin addini.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng