Tsarabar Juma'a: Siffofin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW

Tsarabar Juma'a: Siffofin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW

Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mutum ne da ke da matukar kima da daraja a duniya baki daya musamman ma musulmai wanda ya rayu sama da shekaru dubu da suka shude a garin Makka da Madina, kasar Saudiyya a yanzu.

Mabiya addinin musulunci dai sun yi imanin cewa shine annabi na karshe kuma shi ne ya zo da alkur'ani mai girma kuma tsarkakke ne dake da cikakkiyar siffa da kamala wajen jiki da kuma halaye masu kyau.

Tsarabar Juma'a: Siffofin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW
Tsarabar Juma'a: Siffofin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Allah ya kama wata mata mai tsanar masu sa hijabi

Ga dai wasu daga cikin siffofin sa nan kamar yadda suka zo a hadissai:

1. Fuskar sa ta daidaita kuma tana da matukar kyaun siffa, Anas Bin Malik ya bayyana fuskar sa da farin wata. A wani kaulin ma yace gaskiya fuskar sa tafi farin wata kyau da kyalli.

2. Manzon Allah SAW dogo ne kuma mai tsayayyen jiki. Ance cikin sa bai turo ba, baya da tumbi.

3. Idanun fiyayyen halitta sun yi matukar halittuwa kuma sun daidaita a fuskar sa. Bakin cikin idon yayi baki sosai, farin idon kuma yayi fari sosai shima.

4. Manzon tsira an ruwaito cewa yana da zazzakar murya kuma yana da dogon wuya wanda yayi daidai da shi.

5. Manzon Allah SAW haka zalika ance fuskar sa cike take da gemu da kuma saje wanda yayi masa matukar kyau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng