Mu komawa Al-Kur’ani da Hadisan Annabi Muhammad SAW - Atiku

Mu komawa Al-Kur’ani da Hadisan Annabi Muhammad SAW - Atiku

- Tsohon Mataimakin Shugaban kasa yayi wata nasihar azumi

- Atiku Abubakar ya nemi jama’a su yawaita karatun AlKur’ani

- ‘Dan siyasar ya kuma yi kira ga jama’a su koma bautar Allah

A jiya ne mu ka ji cewa Mataimakin Shugaban kasar nan daga 1999 zuwa 2007 Alhaji Atiku Abubakar yayi nasiha ga Jama’a kan azumin wannan wata mai albarka na Ramadan ta shafukan sa na sada zumunta.

Mu komawa Al-Kur’ani da Hadisan Annabi Muhammad SAW - Atiku
Atiku ya nemi a yawaita karatun Kur’ani da bibiyar Sunnah

Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya nemi Musulmai a wannan watan mai falala su yi kokari wajen yawaita karatun Al-Kur’ani mai girma. Atiku yace ta haka ne Musulmai za su yi maganin duk matsalolin da ke damun zukatan su.

KU KARANTA: Wani ya fada rijiya ana tsakiyar azumin Ramadan a Kano

Bayan haka kuma tsohon Mataimakin Shugaban kasar yayi kira ga Musulmai su rungumi Hadisan Manzon tsira Annabi Muhammadu SAW. Atiku Abubakar yayi wannan tunatarwar ne ta shafin sa na zumunta na zamani na Tuwita.

Babban ‘Dan siyasar yake tunatar da jama’a game da maganar Manzon Allah Annabi Muhammadu SAW da yace mafi alkhairin Mumini shi ne wanda yake tuna Ubangiji a safe da kuma cikin dare musamman a wannan Wata na Ramadan.

A jiyan ne kuma Muhammadu Buhari ya gana da ‘Yan kungiyar BSO na Magoya bayan sa a fadar Shugaban kasar da ke Aso Villa inda ya tattauna da su kan batutuwan da su ka shafi halin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel