Kotun ECOWAS Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Dokar Batanci ga Ma’aiki a Kano

Kotun ECOWAS Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Dokar Batanci ga Ma’aiki a Kano

  • Kotun ECOWAS ta yanke hukunci cewa dokokin batanci na jihar Kano sun saba wa hakkokin dan Adam na duniya
  • Ta bayyana cewa sassan doka na laifuffuka da na dokokin da Sharia na jihar Kano sun tauye ’yancin fadin albarkacin baki
  • Ta kuma umurci gwamnatin Najeriya ta soke ko ta gyara wadannan dokokin da suka saba wa tsarin doka na duniya
  • Kotun ta ce dokokin sun haddasa kama mutane ba bisa ka’ida ba, da tsare su har abada, da hukuncin kisa wanda ya saba musu hakki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kotun Shari’a ta ECOWAS ta yanke hukunci kan dokar batanci da ake amfani da ita a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Kotun ta ce dokokin batanci na jihar Kano sun ci karo da ka’idojin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da ake da su.

Kara karanta wannan

Sabuwar wakar caccakar Tinubu ta tayar da kura a Najeriya

Kotun ECOWAS ta kalubalnci dokar batanci a Kano
Kotun ECOWAS ta bukaci soke dokokin batanci a Kano da kuma Najeriya. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Musabbabin maka gwamnatin Kano a kotun ECOWAS

Wata kungiya mai suna 'Expression Now Human Rights Initiative' ce ta shigar da kara, tana cewa dokokin sun haddasa kama mutane ba bisa ka’ida ba da tsare su har abada, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta zargi dokokin da hana mutane ’yancin fadin albarkacin bakinsu tare da haifar da farmaki da kashe-kashe daga mutane bisa zargin batanci.

Kotun ta bayyana cewa sashe na 210 na laifuffuka da hukunci da sashe na 382(b) na dokokin Sharia na jihar Kano sun saba da doka.

Kotun ECOWAS ta ce dokar batanci ta yi tsanani

Kotun ta ce sashe na 210 ba ya bayyana a fili abin da ake nufi da cin zarafin addini, lamarin da ya sabawa ka’ida.

Sashe na 382(b) wanda ke hukuncin kisa ga wanda ya zagi Annabi Muhammad (SAW), kotun ta ce hukunci ne mai tsanani a cikin tsarin dimokiradiyya.

Duk da haka, kotun ta ce babu isasshen shaidar da ke tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta kasa hana kashe-kashe kan zargin batanci.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yaɓawa kamfanonin wuta 8 tara saboda zaluntar ƴan Najeriya

Kotun ECOWAS ta bukaci garambawul a dokar batanci a Kano
Kotun ECOWAS ta koka kan dokar batanci a Kano inda ta bukaci sauya mata tsari. Hoto: @ecowas_cedeao, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Umarnin da kotun ta ba gwamnatin Najeriya

Kotun ta umurci gwamnatin Najeriya da ta soke ko ta gyara wadannan dokoki domin su yi daidai da ka’idar dokokin kare hakkin dan Adam.

Ta ce tana da ikon sauraron karar, kuma ta bayyana cewa karar ta dace saboda ta shafi ’yancin fadin albarkacin baki, Premium Times ta ruwaito.

Daga bisani, kotun ta bukaci gwamnati ta cire dokokin da suka sabawa sashe na 9(2) na 'African Charter' da sauran yarjejeniyoyin kasa da kasa.

Kotun ECOWAS ta ci tarar gwamnatin tarayya

Mun ba ku labarin cewa bayan zargin Gwamnatin Tarayya da take hakkin dan Adam a zanga-zangar EndSARS, kotun kungiyar ECOWAS ta gano laifuffukan gwamnati.

Kotun ta bayyana cewa gwamnatin ta ci zarafi tare da take hakkin masu zanga-zangar EndSARS da aka yi a shekarar 2020 wanda ya tayar da hankula a fadin kasar musamman a Kudanci.

Kotun ta umarci gwamnatin ta biya kowa daga cikin wadanda suka shigar da korafin N2m a matsayin diyyar take musu hakki ba tare da bata wani lokaci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng