Da Duminsa: Kotun ECOWAS Ta Dakatar da Gwamnatin Buhari Daga Cafke Yan Najeriya Dake Hawa Twitter
- Kotun ECOWAS ta dakatar da gwamnatin shugaba Buhari daga hukunta yan Najeriya waɗanda suka hau twitter
- Wannan ya biyo bayan ƙarar da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam SERAP ta shigar gaban kotun tana ƙalubalantar matakin FG
- A ranar Jumu'a, 4 ga watan Yuni, ministan yaɗa labarai ya sanar da hana amfani da twitter a Najeriya
Kotun ƙungiyar ƙasashen nahiyar Africa (ECOWAS) ta bayyana wata doka da ta hana shugaban ƙasa Buhari ko wani daga cikin gwamnatinsa hukunta yan Najeriya kan amfani da twitter, kamar yadda the cable ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Buhari Ya Jaddada
Kotun ta ɗau wannan matakin ne bayan ƙarar gwamnatin tarayya da aka shigar gaban ta, wanda ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam SERAP da wasu yan Najeriya 176 suka yi.
SERAP ta garzaya gaban kotun ECOWAS ne tana neman a bi wa yan Najeriya haƙƙinsu biyo bayan matakin gwamnatin Buhari na hana hawa twitter.
A ranar 4 ga watan Yuni FG ta hana amfani da twitter a Najeriya
Minsitan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya sanar da hana amfani da twitter har sai baba ta gani a Najeriya ranar 4 ga watan Yuni.
A cewar ministan: "Kamfanin sada zumunta na twitter yana gudanar da wasu ayyuka da suke bazata ga kasancewar Najeriya ɗaya."
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya
Antoni Janar, Abubakar Malami, ya bada umarnin hukunta duk wani ɗan Najeriya da aka kama yana amfani da twitter bayan an hana.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki
Yan bindigan da suka yi awon gaba da ɗalibai a FGC Birnin Yauri sun saki hotunan waɗanda suka kama, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
A makon da ya gabata ne maharan suka dira makarantar sakandiren, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai.
Asali: Legit.ng