Kotun ECOWAS ta ci tarar Gwamnatin Tarayya N50 kan danne hakkin Alkalin Abuja

Kotun ECOWAS ta ci tarar Gwamnatin Tarayya N50 kan danne hakkin Alkalin Abuja

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, an ci tarar gwamnatin tarayyar Najeriya Naira hamsin kacal yayin da wata kotun ECOWAS ta kama ta da laifin danne hakkin wani babban Alkalin Babbar Kotu a Abuja.

Kotun ta kungiyar kasashen Yammacin Afrika da ke zamanta a garin Abuja, ta umarci gwamnatin Tarayya ta biya Mai Shari'a S.E Aladetoyinbo diyyar danne masa hakki.

A karar mai lamba ECW/CCJ/APP/27/18 wadda Mai Shari'a Aladetoyinbo ya shigar, ya yi ikirarin cewa, hukumar NJC da ke sa ido kan al'amurran shari'a a Najeriya ta keta hakkinsa na 'yanci daga azabtarwa.

Alkalin ya ce Hukumar NJC wadda ta ke yi wa gwamnatin tarayyar Najeriya wakilci, ta danne masa hakkin ne sakamakon wallafa wata wasika ta gargadi da tayi a kansa.

Ya kuma yi ikirarin cewa NJC ta keta hakkin sa na 'yancin sauraren korafi saboda kwamitin da ta kafa bai biyo ta hanyar da ta dace ba kuma bai cancanta ba.

Kotun ECOWAS ta ci tarar Gwamnatin Tarayya N50 kan danne hakkin Alkalin Abuja
Kotun ECOWAS ta ci tarar Gwamnatin Tarayya N50 kan danne hakkin Alkalin Abuja
Asali: UGC

Mai Shari'a Aladetoyinbo ya zayyana cewa, gargadin da NJC ta yi masa ya biyo bayan wani korafi na nuna rashin jin dadi kan hukuncin wata shari'a da ya zartar a kan rikicin kasa da wasu suka shigar.

Babban Alkalin ya ce kuma daga bisani Kotin koli ta tabbatar da hukuncin shari'ar da ya gabatar

Ya ce Kwamitin da Hukumar NJC ta kafa wanda rashin daidaito ya mamaye shi, bayan jan kunnensa, ya kuma nemi a sanya ido a kansa har na tsawon watanni tara.

Yana mai cewa: "Wannan lamari ya yi matukar muzguna masa kuma ya bata masa suna da zubar masa da mutunci tare da rage masa duk wata kima da martaba wadda ya gina tsawon fiye da shekaru talatin da suka gabata."

Ya roki kotun da ta ba da umarnin a biya shi diyyar N855,625,000 ta bata masa sunan da aka yi da kuma N12,230,750 na asarar da ya yi wajen shigar da kara.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta amince da kudirin buɗe sabbin jami'o'i a Najeriya

Haka kuma ya nemi a tilasta wa Hukumar da ta jefa shi cikin kunci, da ta wallafa wasikar neman afuwarsa a jaridu da sauran kafofin sadarwa.

Yayin zartar da hukunci a ranar Laraba, tawagar Alkalai uku bisa jagorancin Edward Amoako Asante, ta goyin bayan duk wasu hujjoji da dalilai da ya gabatar mata.

Sai dai kotun ta ce ya gaza bayar da shaidar lahani ko azabtarwa da wasikar Hukumar NJC ta yi masa, inda ta yanke hukuncin a biya shi diyyar N50 kacal kan keta masa hakkin sa na 'yancin sauraron korafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel