Gwamnati Ta Yaɓawa Kamfanonin Wuta 8 Tara saboda Zaluntar Ƴan Najeriya

Gwamnati Ta Yaɓawa Kamfanonin Wuta 8 Tara saboda Zaluntar Ƴan Najeriya

  • Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta fusata da abin da ta bayyana a matsayin cutar abokan cinikayya da kamfanonin wuta ke yi
  • Wannan ta sa hukumar daukar mataki, kuma ta ci tarar kamfanonin raba wuta takwas kudi har Naira miliyan 628.03 saboda karya doka
  • Kamfanonin da aka ci tarar su, sun hada da Abuja, Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano da Yola, wadanda suka caji abokan huldarsu fiye da kima

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta dauki matakin hukunta wasu daga cikin manyan kamfanonin raba wutar lantarki a kasar nan.

NERC ta dauki matakin ne sakamakon saba dokar da ta kayyade yadda za a caji abokan ciniki da ba su da mita yawan kudin wuta da za su biya.

Kara karanta wannan

Sabuwar wakar caccakar Tinubu ta tayar da kura a Najeriya

Transmission Company of Nigeria
An ci tarar kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa NERC ta ce kamfanonin sun ci gaba da cajin abokan ciniki fiye da kima, lamarin da ya saba da dokokin da hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce kamfanonin da tarar ta shafa sun hada da wadanda ke ba da wuta a Abuja, Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano da Yola.

NERC ta hukunta kamfanonin wutar lantarki

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa hukumar ta ce hukuncin da ta dauka yana bisa tanadin Sashe na 34 (1)(d) na dokar wutar lantarki ta shekarar 2023.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Za a iya tunawa cewa a shekarar 2020, hukumar ta fitar da wata doka kan kayyade cajin da ake yi wa abokan ciniki da ba su da mita (Dokar NERC/197/2020), tare da fitar da adadin kudin wuta da ya kamata a rika caji kowane wata, domin daidaita lissafin da ake yi wa wadanda ba su da mita da yadda ake caji ga wadanda ke da mita a layin wuta daya.”

Kara karanta wannan

Najeriya ta hada kai da kasar Japan domin tallafawa manoma 500,000

“Binciken da hukumar ta yi kan yadda kamfanonin suka caji abokan ciniki da ba su da mita daga watan Yuli zuwa Satumba 2024 (shekara ta 2024/Q3) ya nuna cewa ba su bi ka’idar adadin da aka kayyade ba.”

Nawa NERC ta ci tarar kamfanonin wutar lantarki?

Sakamakon haka, hukumar NERC ta ce ta ci tarar wadannan kamfanoni har Naira miliyan 628.03, wato 5% na jimillar kudin da suka yi caji fiye da kima.

Hukumar ta kuma bukaci kamfanonin su maido da hakkokin abokan ciniki da abin ya shafa ta hanyar rage musu kudi cikin lissafin watan Afrilu, wanda za a kammala zuwa ranar 15 ga Mayu, 2025.

lantarki
Ana zargin kamfanonin rarraba hasken wuta da zaluntar 'yan Najeriya Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: UGC

NERC ta sake jaddada kudirinta na ganin cewa dokokin da ta kafa ana bin su yadda ya kamata da kuma kare hakkokin masu amfani da wutar lantarki a cikin tsarin wutar lantarki na Najeriya (NESI).

Abuja: An samu matsalar wutar lantarki

Kara karanta wannan

An buga asara a Kano da mummunar gobara ta tashi a kasuwar Gandun Albasa

A wani labarin kuma, kun ji yadda aka samu tangardar wutar lantarki a babban birnin tarayya, Abuja, sakamakon wata matsala da ta taso daga layukan rarraba wuta na kamfanin AEDC.

Matsalar ta hana wuta karasa wa wasu sassa na Abuja, ciki har da Fadar Shugaban kasa, lamarin da ya jawo hankulan jama'a da dama, duba da wuraren da abun ya shafa.

Amma kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya bayar da tabbacin cewa Injiniyoyinsa sun yi abin da ya dace wajen tabbatar da an gyara wutar domin cire jama'a daga cikin duhu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng