Daminar Bana: Gwamnatin Najeriya Ta Fadi Jihohin da za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

Daminar Bana: Gwamnatin Najeriya Ta Fadi Jihohin da za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana yiwuwar ambaliya a garuruwa 1,249 a kananan hukumomi 176 da ke cikin jihohi 30 da birnin tarayya Abuja
  • Ministan ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ya ce sauyin yanayi na kara haddasa ambaliya, wanda zai shafi sana'o'i, muhalli da zirga-zirgar ruwa
  • Rahoton NIHSA na 2025 ya lissafa jihohi 30 da ambaliyar ruwan za ta shafa da suka hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra da Bauchi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da yiwuwar ambaliya a garuruwa 1,249 a cikin kananan hukumomi 176 da ke jihohi 30 da birnin tarayya Abuja.

Ministan albarkatun ruwa da tsabtace muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton hasashen ambaliyar ruwa na 2025 a Abuja.

Ministan ruwa da tsaftar muhalli ya yi magana kan ambaliyar ruwa a jihohi 30 a 2025
Gwamnatin tarayya ta lissafa jihohi 30 da za a fuskanci ambaliyar ruwa a 2025. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Getty Images

Jihohi 30 da ambaliyar ruwa za ta shafa a 2025

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Zariya da wani magidanci ya kashe ɗan uwansa da duka

Rahoton da aka gabatar ya fito ne daga hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIHSA) a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, 2025, a cewar jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin da ke cikin hadarin ambaliyar ruwa a daminar bana sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue da Borno.

Sauran jihohin su ne; Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos da Nasarawa.

Har ila yau akwai Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da babban birnin tarayya, Abuja.

Abin da ke haddasa ambaliyar ruwa a Najeriya

Ministan ya nuna damuwa kan cewa ambaliyar ruwa na daga cikin manyan masifun da ke addabar Najeriya a duk shekara.

Farfesa Joseph ya ce sauyin yanayi yana kara tsananta yawan ambaliya da illarta ga muhalli da rayuwar al’ummar Najeriya.

An yi hasashen cewa ambaliyar ruwa a bana za ta shafi yankunan bakin teku da koguna kamar Bayelsa, Legas da Cross River.

Kara karanta wannan

Alkali ya sha da kyar bayan yan ta'adda sun yi ram da shi a Katsina

Farfesa Joseph ya ce hakan zai yi matukar shafar sana'ar kamun kifi, rayuwar namun daji da zirga-zirga a kan ruwa a wadannan yankuna.

Yadda ambaliyar za ta shiga manyan birane

Rahoton hukumar NIHSA na 2025 ya nuna cewa garuruwa 2,187 a cikin kananan hukumomi 293 suna cikin matsakaicin hadarin ambaliya.

Ana sa ran ambaliyar za ta shafi manyan birane sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake sa ran zai sauka da kuma rashin kula da magudanan ruwa.

Ministan ya ce ambaliya na iya takaituwa idan aka samu shiri na musamman kafin saukar ruwan da kuma gina ababen more rayuwa da suka dace.

An bayyana amfanin rahoton AFO na 2025

Ministan albarkatun ruwa ya yi magana kan yiwuwar ambaliya a jihohi 30 da Abuja
Ministan albarkatun ruwa, Joseph Utsev, ya fadi hanyoyin takaita ambaliya a Najeriya. Hoto: @FMINONigeria
Asali: Facebook

A jawabinsa, babban sakatare a ma'aikatar ruwa da tsaftar muhalli, Richard Pheelangwah ya bukaci hukumomi su dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyar al'umma.

A cewarsa, bayanan da ke kunshe a cikin rahoton ambaliyar, ba wai iya hasashe ne na lambobi ba, a'a, rahoto ne da zai nusar da muhimmancin daukar matakai kan ambaliyar.

Kara karanta wannan

Farkon Damina: NiMet ta fadi jihohi 12 da za a sheka ruwan saman kwanaki 3

Shugaban hukumar NIHSA, Umar Mohammed, ya ce wannan hasashe ya fi na baya saboda ya gano al’ummomin da ke cikin hadari tun wuri.

Ya ce sababbin fasahohi da hadin gwiwar hukumomi sun taimaka wajen inganta wannan rahoto na AFO 2025, wanda zai taimaka kare kasa daga ambaliya ta hanyar ilimi da kimiyya.

Jihohi da za a yi kwana 3 ana ruwan sama

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen saukar ruwan sama mai karfi a jihohi shida na Kudu, ciki har da Edo.

NiMet ta bayyana cewa daga Laraba 9 zuwa Juma’a 11 ga Afrilu, 2025, ana sa ran ambaliya mai sauki a wasu sassa na kasar.

Jihohin da za su fuskanci ruwan sama mai karfi da iska sun hada da Edo da Akwa Ibom, yayin da za a yi yayyafi a Legas, Abia da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng