Wani farfesa ya bayyana Dalilan dake haddasa Ambaliyar ruwa a Jihar Legas

Wani farfesa ya bayyana Dalilan dake haddasa Ambaliyar ruwa a Jihar Legas

Sakacin gwamnatin jihar legas game da gine-ginen bakin ruwa na daga abubuwan da suke sabbaba ambaliyar ruwa

A yayinda wasu ke ganin kuntatuwa da damuwar yawan ruwa a yankunan tsibirin Legas, a wani bangare guda kuma masu kasuwancin dake da alaka da ruwan sama suna maraba da farin ciki da hakan

Ga mazaunin garin legas yanzu, musamman na kan tsibiri akwai bukatar kasancewa cikin shiri a ko yaushe don tarar zuwan ruwan sama a lokacinsa.

A satin da ya gabata Legit.ng ta ruwaito tafka ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi wanda ya sababar da malara kwalbatoci ,cin gidaje da ambaliyar teku a yankuna da dama a legas, To amma ko menene takamaiman abinda ke janyo ambaliya da malalar ruwa daga kwalbatoci a garin Legas?

Wani farfesa ya Bayyana Masu haddasa Ambaliyar ruwa a tsuburin Legas
Malalar ambaliyar ruwa a Legas

Dukda cewa ambaliyar ruwan sama a bangarori dayawa na duniya ba bakon abu bane amma na Legas nada alaka da sakaci da rashin kulawar gwamnatin jihar daga magance ire-iren abubuwa haka da masu alaka dasu.

KU KARANTA: Ruwan sama: Jama'a na cikin hadari a Najeriya - Inji Farfesa Sani Mashi

Farfesa Benjamin Akpati na makarantar (Nigeria Institute of Oceanography and Marine Research) ya bada bayanai a ciki kuma yayi jan kunne da gargadin cewa mazauna garin Legas da gwamnatin legas nada hannu a cikin wannan lamari ta hanyar fada gine gine da cunkushesu a farfajiyar yankin kasar legas musamman ma bai-bakin rafurfuka da teku, asalin tsarin Legas ba akan yanda take yanzu bane.amma babu wanda ya bada kunnen sauraro gameda gargadin da su kwararrun ilimin yanayin sukeyi.

Legit.ng ta sake nakalto farfesan a tuni da yayi da jan hankali tare da rokon gwamnatin jihar da ta waiwayi tsare-tsaren ta na gine-gine a jihar, da kuma karfafa lura da sanya ido a sababbin gine gine da akeyi a yankunan da hakan yafi aukuwa.

A Najeriya dai baki daya, dayawa daga guraren dake tsibiraine a da sun riga sun tsunduma cikin ruwa sakamakon rashi yin abin da ya kamata gameda lamurran yankunan tekun kasar.

ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng