An Shiga Tashin Hankali a Zariya da Wani Magidanci Ya Kashe Ɗan Uwansa da Duka

An Shiga Tashin Hankali a Zariya da Wani Magidanci Ya Kashe Ɗan Uwansa da Duka

  • A Zariya, wani rikici tsakanin 'yan uwa ya rikide zuwa kisan kai, inda Abubakar Aminu ya lakadawa kaninsa Sani Yusuf dukan mutuwa
  • An garzaya da marigayin zuwa asibitin ABUTH Shika, a nan aka tabbatar da mutuwarsa, yayin da aka ce Abubakar ya tsere daga gari
  • A jihar Neja kuwa, an kama mutane shida da ake zargi da kashe Alhassan Yakubu saboda zargin satar waya a karamar hukumar Agwara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - An shiga tashin hankali a birnin Zariya yayin da wani magidanci, Abubakar Aminu ya kashe dan uwansa, ta hanyar lakada masa dukan tsiya.

An rahoto cewa, Abubakar, ya yi wa kaninsa Sani Yusuf, mai shekaru 50 dukan kawo wuka, lamarin da ya yi ajalinsa a ranar 4 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

'Arewa ta hada kai da Kudu maso Gabas': An ji dabarar kwace mulki daga hannun Tinubu

Majiyoyi sun magantu da wani magidanci ya kashe dan uwansa a Zariya, jihar Kaduna
'Yan sanda sun fara farautar Mallam Abubakar kan zargin kashe dan uwansa a Zariya. Hoto: @Zazzau_Emirate
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya fitar da rahoton a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magidanci ya kashe dan uwansa da duka a Zariya

A cewar bayanan da wani mutumi ya bayar, Abubakar, mai shekaru 53, ya farmaki Mallam Sani a gidansu da ke Unguwar Rimintsiwa, cikin Zariya.

Rahoton ya nuna cewa an garzaya da Mallam Sani zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika (ABUTH) domin ceto rayuwarsa.

Sai dai likitocin da suka duba shi, sun tabbatar da mutuwarsa da misalin karfe 4:50 na safiyar ranar Alhamis, 10 ga watan Afrilu, 2025.

An ce a lokacin da Mallam Sani ya ke kwance a asibitin, jikinsa ya yi tsanani sosai, kuma dukan da dan uwansa ya yi masa ne ya zama silar ajalinsa.

'Yan sanda sun fara farautar magidancin

An rahoto cewa iyalan Mallam Sani sun yi masa sutura tare da binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

A halin da ake ciki, rundunar 'yan sanda ta fara neman Abubakar Aminu ruwa a jallo, sakamakon ya tsere daga yankin bayan abin da ya faru.

Rahoton ya ce jami'an 'yan sanda sun baza komarsu a lungu da sakunan birnin Zariya da ma kewaye, domin cafko Mallam Abubakar.

An ce jami'an tsaron suna kallon mutuwar Mallam Sani a matsayin kisan kai, kuma ana bincike don gano musabbabin rigimar ta su da ta kai ga ajalinsa.

An kama mutane 6 kan zargin kisan kai

Wannan na zuwa ne yayin da aka rahoto cewa 'yan sanda a jihar Neja sun yi nasarar kama wasu mutane shida da ake zargi da kashe wani mutumi.

An ce mutanen shida da aka kama ne ake zargin sun lakawa wani Alhassan Yakubu dukan tsiya har suka kashe shi saboda zargin ya saci wayoyin salula a karamar hukumar Agwara.

Makama, a rahoton da ya fitar a shafinsa na X, ya ce lamarin ya faru a ranar 8 ga Afrilu, yayin da wani Alhaji Dan'umma ya kai rahoton ofishin 'yan sandan Agwara cewar wasu mutane sun lakadawa Alhassan dukan kawo wuka kan zargin satar waya.

Kara karanta wannan

'Inyamurai sun rufe shaguna': Halin da ake ciki a Sokoto kan kisan Hausawa a Edo

An jero mutane 6 da aka kama a Neja

Rundunar 'yan sanda ta dukufa wajen bincike silar mutuwar Mallam Sani a Zariya da wani Alhassan a Neja
'Yan sanda na binciken yadda wasu mutane shida suka kashe wani matashi a Neja. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Wadanda ake zargin sun hada da; Abu Dogo, Babangida Iro, Mustapha Iro, Abdulmajid Anaruwa, Kamal Anaruwa, and Nurudeen Fulani, dukansu mazauna Agwara.

An ce 'yan sanda sun yi gaggawar isa wurin da abin ya faru, inda suka garzaya da Alhassan babban asibitin Agwara, wanda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Majiyoyi daga 'yan sanda sun shaida cewa wadanda ake zargin yanzu haka na tsare, yayin da rundunar ke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Wani ya kashe dan uwansa a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sanda ta cafke wani Yakubu Adamu, mazaunin kauyen Kumbi da ke karamar hukumar Kirfi, jihar Bauchi.

An ce 'yan sanda sun cafke Yakubu ne bisa zargin ya kashe dan uwansa, Yayaji Abubakar, ta hanyar soke shi, da niyyar mallakar babur dinsa.

Kakakin yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng