Birnin ilmi: Shahararrun manyan-manyan makarantu fiye da 10 da ake da su a Zaria

Birnin ilmi: Shahararrun manyan-manyan makarantu fiye da 10 da ake da su a Zaria

- Tun ba yau ba, ana yi wa kasar Zazzau da kirari cewa Zaria; Birnin ilmi

- Akwai makarantun gaba da sakandare rututu a garin Zaria a halin yanzu

- Daga ciki akwai jami’ar ABU Zaria har da makarantar koyon tukin jirgi

Tun fil azal a tarihi, kasar Zazzau ta yi fice da neman ilmi na addinin musulunci tun kafin Turawa su tare da nufin yin mulkin mallaka a Najeriya.

Zariya na cikin garuruwan da su ka fi ko ina yawan makarantu, musamman jami’o’i, da sauran na-gaba da sakandare a Najeriya da yammacin Afrika.

Kwanakin baya Daily Trust ta kawo abin da ya jawo tasirin wadannan makarantu. Legit.ng Hausa ta kawo maku wasu kadan daga cikin makarantun:

1. ABU Zaria

A Oktoban 1962 Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto) ya kafa jami’ar farko a Arewacin Najeriya. ABU Zaria ta na cikin jami’a mafi girma a fadin Afrika.

2. Nigerian College of Aviation Technology (NCAT)

Makarantar nan ta koyon tukin jirgin sama watau NCAT ta na nan a garin Zaria. A 1964 aka kafa makarantar da ake koyon tuki, gyara da aikin jiragen sama.

3. Nigerian Institute of Transport Technology (NITT)

Haka zalika makarantar koyon fasahar tuki ta kasa ta NITT ta na Zaria. An kafa wannan makaranta ne a 1986 domin kawo karshen matsalar zirga-zirga a tituna.

KU KARANTA: Kadarorina na saida, mu ka tura Matasa kasar waje - Kwankwaso

4. Federal College of Education (FCE)

Makarantar tarayya ta koyon aikin malanta ta na wannan gari na Zaria. An kafa FCE ne da sunan makarantar ATC domin horas da manyan malamai a 1962.

5. Centre for Energy Research and Training (CERT)

Tsohon shugaban jami’ar ABU Zariya, Farfesa Iya Abubakar ya kawo shawarar a kafa cibiyar CERT da aka kafa domin ilmin nukiliya, tun ta na CENTECH.

6. National Research Institute for Chemical Technology (NARICT)

NARICT cibiya ce wanda ma’aikatar tarayya ta kimiyya da fasaha ta kafa a Zariya domin a rika amfani da sinadarai wajen kirkirar kayan da za su amfani al’umma.

7. Nigerian Institute of Leather and Science Technology (NILEST)

A shekarar 1964 ne aka kirkiri makarantar NILEST da sunan ides and Skin Demonstration and Training Project (HSDP) domin koyar da ilmin sarrafa ledoji da fatu.

8. Ahmadu Bello University Teaching Hospital (ABUTH)

A garin Zariya ne ake da asibitin koyar da aikin likitanci na ABUTH. Ma’aikatar lafiya ta kafa wannan asibiti da malaman lafiya su ke samun horaswa a Najeriya.

Birnin ilmi: Shahararrun manyan-manyan makarantu fiye da 10 da ake da su a Zaria
Wasu makarantun Zariya Hoto: legit.ng
Source: UGC

KU KARANTA: Alkali ya bada dama Malamai su yi zama da Abduljabbar Kabara

9. Instistute of Agricultural Research (IAR)

Cibiyar aikin gona ta IAR ta kai shekara kusan 100 a garin na Zaria. Wannan cibiya ta na taimaka wa wajen horas da malaman noma tare da jami’ar ABU Zaria.

10. Division of Agricultural colleges

Makarantar nan ta DAC wanda ake koyar da bangarori daban-dabam na ilmin gona ta na wannan gari. Makarantar ta dade na bada shaidar satifiket da difloma.

11. Nuhu Bamalli Polytechnic

Makarantar nan ta koyon aiki ta Nuhu Bamalli Polytechnic ta na Zaria. A cikin wannan jeri, ta na cikin manyan makarantun da gwamnatin jihar Kaduna ta mallaka.

12. Ameer Shehu Idris College of Advanced Studies

Akwai makarantar nan ta Ameer Shehu Idris College of Advanced Studies a wannan gari mai tarihi. Ana horas da dalibai da ilmin NCE da kuma Difloma.

A kusa da garin na Zariya akwai makarantar Shehu Idris College of Health Science & Technology a Makarfi wanda ake koyar da ilmin aikin ungunzoma, jinya da asibiti

A garin na Zariya ne ake da hukumomi da ma’aikatu irinsu National Board for Arabic & Islamic Studies (NBAIS), National Animal Production Research Institute (NAPRI), da National Agricultural Extension Research and Liaison Services (NAERLS)

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit Newspaper

Online view pixel