Rashin Tsaro: Sanatan Borno Ya Taso Ministan Tinubu a gaba kan Sukar Gwamna Zulum
- Kaka Shehu Lawan bai ji daɗin maganganun ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ba kan matsalar rashin tsaro a jihar Borno
- Sanata Kaka Lawan wanda yake wakiltar Borno ta Tsakiya, ya shawarci ministan da ya daina siyasantar da matsalar Boko Haram
- Sanatan ya ƙalubalanci ministan ya je birnin Maiduguri domin ji daga bakin mutanen da ke da alhaki kan samar da tsaro a Borno
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sanata Kaka Shehu Lawan (APC Borno ta Tsakiya) ya yi wa ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, martani kan matsalar rashin tsaro a Borno.
Sanata Kaka Shehu Lawan ya shawarci ministan da ya mai da hankali wajen inganta martabar Najeriya, maimakon siyasantar da matsalar tsaro.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum ya koka kan rashin tsaro
Idan ba a manta ba a ranar Talata, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jawo hankalin gwamnatin Tarayya kan matsalar tsaro, ya ce Borno na samun koma baya kan hare-haren ƴan Boko Haram.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Mohammed Idris ya fitar a ranar Laraba, an ce ya saɓa da iƙirarin Gwamna Zulum.
Ana zargin yana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci da ƴan bindiga a faɗin ƙasar nan.
Sanatan Borno ya caccaki ministan labarai
A martaninsa, Sanata Lawan ya buƙaci ministan da ya yi koyi da tsofaffin ministocin yaɗa labarai da suka gabace shi wajen ɗaga sunan gwamnati maimakon siyasantar da matsalolim jama'a.
Sai dai an ji cewa Mohammed Idris ya musanta cewa ya yi watsi da zancen gwamnatin Zulum.

Asali: Facebook
"Maimakon tallata manufofi da shirye-shiryen wannan gwamnati ta Shugaba Tinubu, abin mamaki ne yadda ministan ya zaɓi siyasantar da batun tsaro da rikicin Boko Haram da ya addabi jama’ar Borno da Arewa maso Gabas."
“Maganganun da ministan ya yi wa gwamnan jihar Borno kan taron tsaron da aka gudanar tare da shugabannin tsaro da masu sarautun gargajiya ciki har da Shehun Borno, Dr. Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi, abin takaici ne da rashin girmamawa.”
"Bai kamata ministan da ke Abuja ya mayar da martani ga babban jami’in tsaro na jiha wanda ke karɓar rahotanni kai-tsaye daga hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya ba."
“Tun daga shekarar 2019, Gwamna Zulum na ƙoƙarin haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen yaƙi da ƴan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran laifuka a jihar."
“Ina ƙalubalantar ministan da ya zo Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya gana da dakarun da ke fagen fama, Gwamna Zulum da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro kafin ya fitar da irin wannan sanarwa."
"Abin dariya ne cewa ko sau ɗaya ministan bai taba nuna tausayinsa ga gwamnatin da al’ummar jihar Borno ba kan hare-haren Boko Haram da kisan mutane da ake fama da su a yankin."
- Sanata Kaka Shehu Lawan
Ƴan Boko Haram sun farmaki tawagar Zulum
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun farmaki ayarin tawagar Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun farmaki tawagar gwamnan lokacin da suke dawowa daga garin Biu bayan ƙaddamar da wasu ayyuka.
Jami'an tsaron da ke cikin ayarin tawagar gwamnan sun samu nasarar daƙile harin bayan sun yi musayar wuta da wadannan miyagu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng