Kungiyar Izala ta Nada Sababbin Mukamai tare da Maye Gurbin Sheikh Jingir

Kungiyar Izala ta Nada Sababbin Mukamai tare da Maye Gurbin Sheikh Jingir

  • Majalisar Malaman Izala ta tabbatar da Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na ƙasa II
  • Shugaban majalisar, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya kafa kwamiti domin cike gibin da marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir ya bari
  • Kungiyar ta fitar da bayani kan kwamitocin fatawa, zakka da kuma harkokin matasa domin inganta tafiyar addinin Musulunci a faɗin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Shugaban Majalisar Malamai ta Ƙasa karkashin ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi nade nade bayan rasuwar Sheikh Saidu Hassan Jingir.

A cikin wani rahoton da ya fito daga hedkwatar Izala da ke Jos, an sanar da kafa sababbin kwamitoci da kuma sabon jagora da zai cike gurbin marigayin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki babban mataki da Amura ta kakaba haraji kan Najeriya

Izala
Izala ta maye gurbin Sheikh Saidu Hassan Jingir. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan nade naden da kungiyar ta yi ne a cikin wani sako da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi, wanda ke shugabantar Majalisar Malamai ta jihar Lagos ne aka tabbatar da shi a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Ƙasa na biyu.

Kwamitocin kungiyar Izala da ayyukansu

An fitar da jerin kwamitoci guda huɗu da aka faɗaɗa, waɗanda za su taimaka wajen tafiyar da manyan ayyuka kamar fatawa, zakka da kula da matasa.

Ofishin mufti na ‘yan agaji

1. Sheikh Barista Aliyu Alhassan Sangei – Shugaba

2. Sheikh Abubakar Usman Mabera – Mataimaki

3. Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi – Mamba

4. Ustaz Salihu Mustapha Bamalli – Sakatare

5. Ustaz Babagana Mallam Kyari – Mamba

Ofishin fatawa na kasa

1. Sheikh Abdulrahman Isa Jega – Shugaba

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana barazanar kwace kujerar Sanatan APC kan Sanata Natasha

2. Imam Ja'afar Hussaini Jos – Mataimaki

3. Ustaz Musa Alburhan – Sakatare

4. Ustaz Adam Gadar Sogai – Mamba

5. Ustaz Abdussalami Abubakar Jega – Mamba

Ofishin sa’in zakka

1. Sheikh Salihu Sulaiman Ningi – Shugaba

2. Imam Bashir Umar Kashere – Mataimaki na 1

3. Dr Hassan Abubakar Dikko – Mataimaki na 2

4. Mallam Abdullahi Salihu – Sakatare

5. Ustaz Ibrahim Muhammad Duguri – Mamba

6. Ardo Mahmud – Mamba

7. Ustaz Saeed Usman Riyom – Mamba

8. Ustaz Kabir Ash-shikawi Zaria – Mamba

9. Alhaji Kasim Yakub B/Ladi – Mamba

Ofishin uban matasa na kasa

1. Sheikh Madu Mustapha Maiduguri – Shugaba

2. Hafiz Dr Shehu Ibrahim Abdullahi Keffi – Mataimaki

3. Ustaz Mujahid Sheikh Saeed Hassan Jingir – Sakatare

Kara karanta wannan

Fubara: An hango Wike na ganawa da 'yan majalisar Rivers a London

4. Alkali Abubakar Salihu Zaria – Mamba

5. Ustaz Salihu Bukar Bauchi – Mamba

Izala
Sheikh Jingir ya yi sababbin nade nade a Izala. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

Majalisar ta yi addu’ar Allah ya jagoranci shugabannin da aka nada, tare da basu basira da ikon tafiyar da amanar da aka daura musu.

An bukaci jagororin Izala su hada kai

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Yusuf Sambo Rigacukun ya yi kira ga shugabannin kungiyar Izala kan hadin kai.

Sheikh Yusuf Sambo ya bukaci Sheikh Sani Yahaya Jingir da Sheikh Abdullahi Bala Lau su hada kansu su yi aiki tare.

Malamin ya ce ba ya fatan ya rasu kungiyar na rabe kamar yadda ya faru da wasu manyan malamansu kamar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng