'Yan Bindiga Sun Sace Babban Malami a Kaduna, 'Yan Sanda, Sojoji Sun Fita Nema
- 'Yan bindiga sun sace malamin Kirista, Fasto Samson Ndah Ali, daga gidansa a safiyar Talata, 8 ga watan Afilu a Mararaba Abro, Kaduna
- Tawagar sojoji, 'yan sanda, da DSS sun fara samame don bin sahun 'yan bindigar da suka sace Fasto Samson da nufin ceto shi cikin aminci
- A wani bangaren, 'yan bindiga sun farmaki kauyen Banga a Kaura Namoda, sun kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun sace malamin addinin Kirista a Kaduna.
An ce 'yan ta'addar sun shiga har cikin gida, sun yi awon gaba da Fasto Samson Ndah Ali, wani malamin Cocin ECWA da ke Mararaba Abro.

Asali: Getty Images
'Yan bindiga sun sace babban fasto a Kaduna
Mai sharhi kan lamuran tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya fitar da rahoton a shafinsa na intanet.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa 'yan bindigar sun farmaki gidan Pasto Samson da ke Mararaba Abro, karamar hukumar Sanga, a jihar Kaduna, a safiyar Talata, 8 ga watan Afilu.
Majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa, 'yan ta'addar dauke da mugayen makamai sun kutsa gidan malamin addinin da misalin karfe 12:45 na dare.
Rahoton ya ce bayan nasarar sace shi daga gidan nasa, 'yan bindigar sun tafi da shi zuwa wani waje da ba a san ko ina ba ne.
An rahoto cewa tawagar hadin gwiwar sojoji, 'yan sand da DSS sun kaddamar da samame da nufin bin sahun 'yan ta'addar don kubutar da Fasto Samson.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaura Namoda
A wani lamarin makamancin wannan, 'yan bindiga sun farmaki kauyen Banga da ke gundumar Kurya Madora, karamar hukumar Kaura Namoda, inda suka kashe mutane da dama.
A rahoton da Makama ya wallafa a shafinsa na X, an ce 'yan ta'addar sun farmaki kauyen da misalin karfe 1:30 na safiyar Laraba, sannan suka bude wuta kan mai uwa da wani.
Bayan sun tabbatar da cewa sun kashe mutane da dama, majiyoyi sun shaida cewa 'yan ta'addar sun kuma yi garkuwa da mutanen kauyen.
An rahoto cewa, mahukunta na shirin zuwa kauyen domin duba irin barnar da 'yan ta'addar suka yi da kuma daukar matakan kubutar da wadanda aka sace.
Zamfara: Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga

Asali: Twitter
Har ila yau, wani rahoto ya nuna cewa dakarun Operation Fansan Yanma sun yi sun yi nasarar dakile harin tawagar dan bindiga Kallamu a Garin Abara, cikin Karamar Hukumar Isa, jihar Zamfara.
Majiyoyin tsaro sun cewa, 'yan bindigar, karkashin Kallamu sun fara taruwa ne tare da yin shiri a yankin Zangon Malam, wanda ke a gabashin Gatawa kafin kai harin.
Rahoton ganin ayyukan 'yan ta'addar ne aka ce ya baiwa ssojojin damar shirya domin tunkarar su, inda suka gwabza fada mai zafi kafin 'yan bindigar suka ranta a na kare.
An ce sojojin sun samu nasarar ceto mutane hudu daga cikin takwas da 'yan bindigar suka sace, amma wani mazaunin garin ya rasu sakamakon harbin bindiga.
Jami'an tsaro sun ceto mutane a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun samu nasarar ceto mutane bakwai da aka sace a jihar Katsina.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ya bayyana cewa jami’an sun tura dauki cikin gaggawa bayan an kai farmaki Dutsinma da Malumfashi.
A Dutsinma, an ceto mata biyar, yayin da a Malumfashi, ‘yan sanda suka ceto Hafsat Amadu da Musa Sani bayan fafatawa da ‘yan ta’addar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng