Dalilin da Zai Sa Mahmud Yakubu Ya Bar Shugabancin INEC a 2025 da Wasu Bayanai
- Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, zai kammala aikinsa a ƙarshen 2025 bayan cikar wa'adinsa na biyu kuma na ƙarshe
- Hukumar da fadar shugaban ƙasa sun karyata jita-jitar da ke yawo cewa an kore shi daga mukaminsa, suka bukaci jama'a su yi watsi da labarin
- Za a nada wanda zai gaje shi ta hanyar bin tsarin doka wanda ya haɗa da naɗin shugaban ƙasa, binciken DSS da tantancewar Majalisar Dattawa
Abuja - Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), zai bar mukaminsa a ƙarshen shekarar 2025 bayan kammala wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe.
Mahmud Yakubu, wanda ya hau kujerar shugabancin INEC a watan Disamba na 2020, ya jagoranci muhimman harkokin zaɓe a tsawon lokacin da shafe zuwa yanzu.

Source: Twitter
Dalilin da zai sauka daga hugabancin INEC
Farfesa Mahmud zai sauka daga kujerar shugaban INEC ne bayan ƙarewar wa'adinsa na biyu saboda babu damar wuce haka kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan
Ana rade radin Tinubu ya tsige shi, Mahmud Yakubu ya saka labule da ma'aikatan INEC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya gaji Farfesa Attahiru Muhammad Jega, wanda ya jagoranci hukumar INEC daga 2010 zuwa 2015.
Mahmud ya jagoranci manyan zaɓuka biyu da suka haɗa da zaɓen 2019 da na 2023, sannan a ƙarƙashinsa ne INEC ta shirya zaɓukan gwamnonin jihohi 11 da ake yi daban.
Yadda Buhari ya naɗa Mahmud Yakubu
Punch ta tattaro cewa a ranar 21 ga watan Oktoba, 2015, gwamnatin Buhari ta amince da naɗin Mahmud Yakubu tare da kwamoshinonin INEC biyar.
Bayan amincewar Majalisar Magabata da Majalisar Dattawa, Mahmud Yakubu ya karɓi ranstuwar kama aiki a matsayin shugaban INEC karon farko ranar 9 ga watan Nuwamba, 2015.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naɗa Yakubu karo na biyu ranar 27 ga watan Oktoba, 2020.
Farfesa Mahmud Yakubu ya kama aiki a wa'adi na biyu na tsawon shekaru biyar ranar 10 ga watan Disamba, 2020 kuma an sa ran sai sauka a watan Disamba, 2025.
Gaskiyar batun tsige Mahmud Yakubu
Hukumar INEC da Fadar Shugaban Ƙasa sun karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Shugaba Bola Tinubu ya sauke Farfesa Mahmud Yakubu daga mukaminsa.
Mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da su, rahoton Vanguard.
Haka kuma, mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya tabbatar cewa duk wata sanarwa game da shugaban INEC za ta fito ne daga sahihan hanyoyin sadarwa na gwamnati
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Bwala ya bayyana saƙon WhatsApp da ke yawo a kafafen sada zumunta na tsige Mahmud Yakubu a matsayin labarin ƙarya.
Matakan da ake bi wajen naɗa shugaban INEC
Wanda zai gaji Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC zai samu wannan matsayi ne bayan tsallake dukkan matakan da aka tanada.
Matakan sun haɗa da haɗa naɗin shugaban ƙasa, tantancewa daga Hukumar Tsaro ta DSS, da kuma nazari da shawarwari daga Majalisar Magabata ta Ƙasa.
Sannan kuma dole za a mika sunansa zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa.
Ana ganin waɗannan matakai dai suna taimaka wa wajen tabbatar da gaskiya da bin doka da ƙa’ida wajen zaɓen sabon shugaban INEC.
Wasu bayanai game da Mahmud Yakubu
Farfesa Mahmood Yakubu shi ne shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Najeriya na yanzu kuma yana kan wa'adinsa na biyu da zai kare a 2025.
A lokacin jagorancinsa, ya ja ragamar shirya zaɓuka ciki har da zaɓukan cike gurbi a jihohi 11 da aka gudanar jim kaɗan bayan ya hau kujerar.
Kafin nada shi a INEC, Farfesa Yakubu ya rike muƙamai a ɓangarenn ilimi da na gudanarwa, inda ya ba da gudunmawa sosai a harkar ilimi da kuma ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
Taƙaitaccen bayani game da INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ita ce ke da alhakin shiryawa da kuma kula da manyan zaɓuka a matakan tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi a Najeriya.
An kafa INEC a shekarar 1998, kuma ita ke da alhakin tabbatar da gudanar da zaɓuka na gaskiya, adalci, da kuma inganci, tare da kiyaye tsarin dimokiradiyya.
Bugu da ƙari, kundin tsarin mulki ya ɗora wa INEC alhakin rijistar masu zaɓe, tsara iyakokin mazaɓu, da kuma sa ido kan ayyukan jam'iyyun siyasa.
Kafin nan nauyin gudanar da zabe ya rataya a kan hukumomi irinsu FEDECO da NEC wadanda aka rika canzawa suna.
INEC na aiki a matsayin wata hukuma mai zaman kanta, wadda take biyayya ga tsarin doka da ƙa'idojin tsarin mulki.
A wasu shekaru da suka gabata, INEC ta ɓullo da sababbin hanyoyi kamar na'urar tantance masu kaɗa kuri'a domin ƙara inganta harkokin zaɓe na gaskiya da inganci.
Hukumar INEC tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban mulkin dimokiradiyya a Najeriya da kuma gyaran tsarin zaɓe.
An fara tururuwar rijistar jam'iyyu a INEC
A wani labarin, kun ji cewa INEC ta bayyana cewa ta samu saƙonnni daga ƙungiyoyi 91 da kw son a masu rijistar zama jam'iyyun siyasa a Najeriya.
Wannan lamari dai na zuwa ne a lokacin da ƴan adawa ke shirye-shiryr ƙulla haɗakar jam'iyyu domin kawar da gwamnatin APC a babban zaɓen 2027.
Sai dai ana ganin wannan yawaitar rijistar sababbin jam'iyyun wata alama ce da ke nuna har yanzi babu haɗin kai a.tsakanin ƴan adawar ƙasar nan
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


