INEC: Jerin duka Shugabannin Zabe 13 da Aka Yi a Tarihin Najeriya tun daga 1958

INEC: Jerin duka Shugabannin Zabe 13 da Aka Yi a Tarihin Najeriya tun daga 1958

  • Mun tattaro jerin wadanda su ka taba rike shugabancin hukumar zabe a Najeriya tun da ake kada kuri'a a kasar nan
  • Attahiru Jega ne bahaushen farko, har yau babu wani bayaraben da ya rike hukumar kamar yadda tarihi ya tabbatar
  • Farfesa Mahmood Yakubu shi ne shugaba na farko da gwamnati ta kara wa’adinsa, ya shafe kusan shekaru 10 a ofis

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba 2025, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da nadin sabon shugaban hukumar zabe na kasa wato INEC.

An amince da nadin Farfesa Joash Amupitan bayan karewar wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya bar ofis a makon nan.

INEC.
Farfesan da zai zama sabon shugaban hukumar INEC Hoto: Joash Ojo Amupitan (SAN)
Source: Facebook

Jaridar nan ta Daily Trust ta ce daukacin majalisar koli ta amince da nadin Farfesan shari'an wanda aka haifa a shekarar 1967.

Tarihin kujerar shugaban INEC a Najeriya

Kara karanta wannan

Najeriya ta karyata bankin duniya kan samun talakawa miliyan 139 a mulkin Tinubu

A tarihi babu shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC (a yanzu) da ya taba rike wannan kujera sau biyu tun daga shekarar 1958 sai a 2020.

Marigayi hugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba Farfesa Mahmood Yakubu, sabon wa’adi, hakan ya ba shi damar kai wa 2025 a INEC.

Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin duka shugabannin hukumar zaben da aka yi a tarihi, tun ana kiranta da hukumar NEC ko kuma FEDECO.

Sunayen shugabannin INEC da aka yi

1. Mr. Ronald Wraith (1958-1963)

2. Eyo Esua (1964-1966)

3. Michael Ani (1978-1980)

4. Victor Ovie-Whiskey (1980-1983)

5. Eme Awa (1987-1989)

6. Humphrey Nwobu Nwosu (1989-1993)

7. Okon Uya (1993-1994)

8. Summer Dagogo-Jack (1994-1998)

9. Ephraim Akpata (1998-2000)

10. Abel Goubadia (2000-2005)

11. Maurice Mmaduakolam Iwu (2005-2010)

12. Attahiru Muhammadu Jega (2010-2015)

13. Mahmood Yakubu (2015-2025)

13. Joash Amupitan (2025-)

INEC.
Tsohon shugaban hukumar zabe ta INEC Hoto: Signal.ng
Source: UGC

Bayani a kan shugabannin INEC da aka yi

  • Ronald Wraith, mutumin Birtaniya shi ne wanda ya fara shirya zabe a Najeriya. Wraith ya na aiki a jami’ar Ibadan aka ba zabe shi domin ya rike hukumar zabe ta kasa a 1958.
  • Eyo Esua ya rike shugabancin hukumar zabe a gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa tsakanin 1964 zuwa 1966. Esua ya na rike da hukumar soji su ka hambarar da gwamnati.
  • Bayan an fara shirin dawo wa mulkin farar hula, aka zabi Michael Ani, wanda ma’aikacin gwamnati ne a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta FEDECO a 1978.
  • A shekarar 1980 shugaban kasa Shehu Shagari ya nada Alkali Victor Ovie-Whiskey ya jagoranci hukumar zabe. Ovie-Whiskey ya rike kujerar FEDECO har zuwa karshen 1983.
  • Farfesa Eme Awa ya zama shugaban hukumar zabe na shekaru kusan biyu daga 1987 zuwa 1989. Eme Awa ya sauke daga kujera ne bayan ya samu sabani da gwamnatin lokacin.
  • Bayan Eme Awa, Ibrahim Babangida ya zabi Farfesa Humphrey Nwobu Nwosu ya maye gurbinsa har 1993. Humphrey Nwosu ne ya jagoranci zaben 1991 da sojoji su ka soke.
  • Mutumin Akwa Ibom. Farfesa Okon Edet Uya shi ne ya karbi ragamar hukumar zabe a 1993. Uya bai iya gudanar da wani babban zabe ba har ya bar gwamnatin Sani Abacha.
  • Cif Summer Karibi Dagogo-Jack ya zama sabon shugaban hukuma zabe ta NEC a 1994 har zuwa 1998. Kafin nan Summer Dagogo-Jack ya yi aiki da Farfesa Humphrey Nwosu.
  • Alkali Ephraim Omorose Ibukun Akpata shi ne ya shirya zaben 1998 da 1999 bayan an dawo farar hula. Tsohon Alkalin babban kotun kolin Najeriyar ya rasu a farko shekarar 2000.
  • Bayan Ephraim Akpata, sai Abel Goubadia ya zama shugaban hukumar INEC a 2000, har 2005 lokacin da Olusegun Obasanjo yake mulki.
  • Farfesa Maurice Mmaduakolam Iwu ne wanda ya rike shugaban hukumar har zuwa 2010. Shi ne ya gudanar da zaben 2007 da ya sha suka a Najeriya.
  • A 2010, gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada Attahiru Muhammadu Jega a matsayin shugaban INEC. Attahiru Muhammadu Jega ya samu damar shirya zaben 2010 da kuma na 2015.

Kara karanta wannan

Farfesa Mahmood: Daga ajiye aiki, kotu ta bada umarni a kamo mata tsohon shugaban INEC

Amupitan zai karbi ragamar INEC

Tun kafin yanzu kun samu labari ana jita-jitar Joash Ojo Amupitan ne ke kan gaba cikin jerin wadanda ake sa ran za su maye gurbin Mahmood Yakubu.

Farfesa Joash Ojo Amupitan mai shekaru 58 masanin shari'a ne wanda ya shafe shekara da shekaru yana karantarwa a jami'ar Jos a jihar Filato.

Farfesan shi ne shugaban farko na INEC da aka yi daga yankin Arewa maso tsakiya kuma shugaba na uku a jere da ya fito daga Arewacin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng