Rai Baƙon Duniya: Musulunci Ya Yi Rashi da Babban Malami Ya Rasu a Birnin Kebbi

Rai Baƙon Duniya: Musulunci Ya Yi Rashi da Babban Malami Ya Rasu a Birnin Kebbi

  • Allah ya karbi rayuwar Imam Bello Jandutsi, babban limamin masallacin Sheikh Abbas Jega da ke jihar Kebbi, a daren Litinin, 7 ga Afrilu 2025
  • Marigayin ya kwashe fiye da shekaru 30 yana limanci, tafsir, da da’awa a cikin masallacin Juma’a na Sheikh Abbas Jega da ke Birnin Kebbi
  • Sanarwa daga kungiyar Izala ta nuna cewa za a yi sallar jana’izar malamin a ranar Talata, da karfe 10:00 na safiya, a masallacin Sheikh Abbas

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Birnin Kebbi - Kungiyar addinin Musulunci ta Izala da ke Najeriya (JIBWIS), ta sake yin babban rashi na malaminta, da aka sanar da rasuwar Imam Bello Jandutsi.

Imam Bello Jandutsi, ya kasance babban malami a Izala, kuma babban limamin masallacin Sheikh Abbas Jega da ke Rafin Atiku, a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Bayan Dusten Tanshi, Pantami ya sanar da rasuwar babban malamin Musulunci

An sanar da rasuwar babban limami a Izala, Imam Bello Jandutse a Birnin Kebbi
Allah ya yi wa malamin Izala, Imam Bello Jandutse rasuwa a Birnin Kebbi. Hoto: Jibwis Kebbi
Asali: Facebook

Malamin Izala, Imam Bello ya rasu a Birnin Kebbi

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin JIBWIS Kebbi na Facebook, an ce Allah ya karbi rayuwar Imam Bello Jandutsi a daren ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta shaida cewa, babban malamin ya shafe fiye da shekaru 30 yana limanci a babban masallacin Juma'a na Sheikh Abbas Jega.

Baya ga limanci, sanarwar ta kuma ce marigayi Imam Bello Jandutsi ya shafe wadannan shekaru yana karantarwa, yin tafsir da da'awa, a masallacin.

An sanya lokacin jana'izar Imam Bello

Sanarwar ta ce Imam Bello Jandutsi ya kasance mutum mai tsantsar tawali'u da kuma kyawun mu'amala.

An shirya gudanar da sallar jana'izar malamin a ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025 a masallacin Juma'a na Sheikh Abbas Jega da ke Rafin Atiku, Birnin Kebbi.

An ce za a gudanar da sallar jana'izar ne da misalin karfe 10:00 na safiya, yayin da sanarwar ta yi addu'a ga mamacin domin Allah ya jikansa da Rahama.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Dutsen Tanshi, an sanar da mutuwar fitaccen Sarki a Kebbi

Mutane sun yi alhinin rasuwar Imam Bello

Musulmi na gudanar da Sallah a jihar Kebbi
Za a gudanar da Sallar Jana'izar Imam Bello Jandutse a Birnin Kebbi. Hoto: Jibwis Kebbi
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattar wasu daga cikin sakonnin ta'aziyya da alhinin da mutane suka aika bayan samun labarin rasuwar Imam Bello:

Abubakar Sadeeq Abu Abdullah:

"Allah ya jikan mallam da Rahama, ya sa Aljannah Firdausi a'ala ce makomarsa.
"Lallai an yi rashi babba, malami mai huduba wacce ta dace da zamani, malam bai damu da abin duniya ba, mutumin kirki, Allah ya haskaka masa kabarinsa don Rahamarsa wadda ta ishi kowa, Allah ya albarkaci iyalansa ya yi musu budi na alkhairi."

Maryam Jafaru:

"Allah sarki, Allah ya ya jikansa ya gafarta masa, ya yi masa Rahma, ya sa Aljanna ce makomarsa, idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da imani."

Abdool-Hakeem Bandiya Sa'ad:

"Mutumin kirki ya rigamu gidan gaskiya, Allah ya ji kan ka da Rahma."

Shafi'u Bello:

"Allah ya jikan shi da Rahama, ya sa Aljannah ce makomarsa da sauran Musulmai baki daya."

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

Saniyellow Sayaya:

"Allah ya gafarta masa, ya ba da hakurin rashinsa."

Haruna Muhammed:

"Wannan babban rashi ne a garemu, Allah ya tausayawa malam, ya karbi kyawawan ayukkansa, ya albarkaci zuri'a."

Duba sanarwar JIBWIS a kasa:

Shugaban malamai a Izala, Jingir, ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Allah ya karbi rayuwar mataimakin shugaban malamai na ƙungiyar Izala ta ƙasa na biyu, Sheikh Saidu Hassan Jingir.

Marigayi Sheikh Saidu ya shafe shekaru da dama yana koyar da addinin Musulunci a sassa daban-daban na ƙasar nan kafin rasuwarsa.

An gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 2:00 na rana bayan sallar Azahar a masallacin Santa, Unguwar Rimi, Jihar Filato a ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng