Janar Tsiga: An Ji Yadda Tsohon Shugaban NYSC Ya Kubuta daga Hannun 'Yan Bindiga

Janar Tsiga: An Ji Yadda Tsohon Shugaban NYSC Ya Kubuta daga Hannun 'Yan Bindiga

  • Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta kasa ta miƙa tsohon shugaban NYSC, Maharazu Tsiga, da wasu mutane 18 da aka ceto ga Nuhu Ribadu
  • Ana ganin kubutar da mutanen 19 wani ci gaba ne a yaƙi da 'yan bindiga, bayan Janar Tsiga ya shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa
  • Nuhu Ribadu ya jinjinawa jami’an tsaro kan nasarar ceto Tsiga da mutane 18, tare da jaddada aniyar gwamnati na inganta yanayin tsaro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta kasa ta miƙa tsohon darakta janar na hukumar NYSC, Maharazu Tsiga ga Nuhu Ribadu a Abuja.

An ce cibiyar NCTC ta mika Janar Tsiga da sauran mutane 18 da aka ceto daga hannun 'yan bindiga ga mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Mun sha azaba': Janar Tsiga ya magantu, ya fadi dabbobin da suke kwana tare da su

Nuhu Ribadu ya magantu da cibyar yaki da ta'addanci ta kasa, ta mika masa Janar Tsiga da wasu mutane 18
Cibyar yaki da ta'addanci ta kasa, ta mika Janar Tsiga da wasu mutane 18 da aka ceto ga Nuhu Ribadu.
Asali: Twitter

An mika Janar Tsiga ga Nuhu Ribadu

Rahoton jaridar Punch ta nuna cewa ceto Tsiga da mutanen 18 alama ce da ke nuna wani ci gaba mai muhimmanci a yaki da masu garkuwa da mutane a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, mun rahoto cewa an sace Janar Tsiga tare da wasu mutane a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025, a garinsu na Tsiga da ke Bakori, jihar Katsina.

Sai dai, Janar Tsiga ya shaki iskar 'yanci a ranar Laraba bayan shafe kwanaki 56 cikin ukuba a hannun masu garkuwa da shi.

Wani rahoton Legit Hausa ya nuna cewa Janar Tsiga ya kubuta ne bayan da iyalansa suka biya kudin fansa da ya kai kimamin Naira miliyan 180.

Yadda aka biya miliyoyin kudi kan Tsiga

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa 'yan bindigar sun fara neman N250m, amma aka daidaita a kan N60m.

Kara karanta wannan

Ruwa ya yi gyara: Gidaje sama da 70 sun yi fata-fata a Filato

Sai dai, bayan an kai masu N60m, sai suka katse sadarwa da iyalan tsohon shugaban NYSC din, sannan daga bisani suka kira waya, suka nemi karin kudi.

Wani daga cikin iyalan Tsiga da ya zanta da jaridar Daily Trust ya ce ba a kara wa 'yan bindigar ko sisin kwabo ba, har zuwa lokacin da aka sako shi.

Amma jaridar ta ce, wata majiya mai tushe ta tabbatar mata da cewa sai da aka biya 'yan bindigar nunki uku na wannan N60m da aka fara kai masu.

Nuhu Ribadu ya jinjinawa jami'an tsaro

Bayan nasarar kubutar Janar Tsiga, cibiyar yaƙi da ta’addanci ta kasa (NTCT) ta garzaya da shi da mutane 18 da aka kubutar da su zuwa ga Nuhu Ribadu.

A yayin da ya karbe su, Nuhu Ribadu ya yabawa kokarin jami’an tsaro da hukumomin leƙen asiri da suka taka rawa wajen kubutar da Tsiga da mutanen 18.

Kara karanta wannan

Karshen wahala: Janar Tsiga ya sami ƴanci bayan watanni 2 a hannun ƴan bindiga

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙara inganta harkokin tsaro tare da tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Ana ganin jawabin na Ribadu, ya nuna cewa jami'an tsaro ne suka kubutar da Janar Tsiga, ba wai ya shaki 'yanci don kudin fansar da aka biya kadai ba.

Mutane sun firgita da aka sace Janar Tsiga

Tun da fari, mun ruwaito cewa, mazauna Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina sun shiga jimami kan sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga.

Sace tsohon shugaban NYSC ya haddasa fargaba a yankin, inda al’umma suka shiga cikin tsoro da damuwa kan tabarbarewar tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna garin na Tsiga sun bar gidajensu saboda tsoron harin 'yan bindiga da ke kara tsananta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng