Yadda Ɗan Sokoto Ya Yi Ridda, Ya Sake Dawowa Musulunci bayan Sanata Ya Tsoma Baki
- Wani mutum mai suna Musa Abubakar, wanda ya yi ridda saboda tsoron ’yan bindiga, ya sake karɓar addinin Musulunci tare da matansa biyu
- Mutumin ya yi ƙaura daga Sokoto zuwa Taraba saboda matsalar tsaro, ya shawo kan matansa su shiga Kiristanci, amma daga baya suka koma Musulunci
- Ality Magatakarda Wamakko ya kafa kwamitin malamai domin faɗakar da Musa game da ridda, kuma kwamitin ya tattauna da shi kan dalilansa
- Musa ya bayyana nadamarsa na barin addinin Musulunci, ya ce zai ci gaba da kasuwanci a Sokoto tare da iyalansa kuma su tsaya kan addinin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Wani mutum mai suna Musa Abubakar, wanda ya sauya addini zuwa Kiristanci sakamakon hare-haren ’yan bindiga, ya sake karɓar Musulunci.
A ranar Asabar 29 ga watan Maris, 2025 ne shi da matansa biyu suka dawo Musulunci bayan ridda da suka yi a baya saboda dalilan tsaro da kuma wahalhalun rayuwa.

Asali: Original
Yadda ɗan Sokoto ya yi ridda zuwa Kiristanci
Rahoton Aminiya ya ce Musa, wanda dan asalin Sabon Birni ne a Sokoto, ya bar garinsu zuwa Taraba domin guje wa barazanar ’yan bindiga da ke yawan kai hare-hare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A can Taraba ne ya shawo kan matansa su sauya addini, amma hakan ya jawo cece-kuce, inda har Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya kafa kwamiti don fahimtar da shi.
Kwamitin da ya kunshi manyan malamai daga Sokoto ya tattauna da Musa, inda ya bayyana dalilin da ya sa ya koma Kiristanci a baya.
Malam Bashir Gidan Kanawa ya ce rashin ilimin addini da kuma matsalar tsaro sun sa Musa ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa wani sabon addini.
Ya ce:
“A Taraba ne aka yi amfani da tallafin kuɗi wajen yaudarar shi zuwa Kiristanci, da yadda aka rinjaye Musa da iyalansa."

Asali: Facebook
Musa ya yi magana kan lamarin
Bayan doguwar tattaunawa da malamai da dangi, Musa ya amince da kuskurensa, ya ce ya yi ridda ne saboda halin da ya shiga, amma yanzu ya dawo.
Musa ya ce:
“A yanzu na koma addinina na asali tare da iyalina, kuma ina nadamar abin da na aikata."
Ya kuma bayyana cewa zai zauna a Sokoto domin ci gaba da sana’arsa, tare da alwashin cewa shi da iyalansa ba za su sake barin Musulunci ba.
A nasa bangaren, wani yayan Musa, Alhaji Adamu, ya ce su kansu ’yan bindiga sun kashe mahaifinsu duk da cewa sun karɓi kuɗin fansa har N9m.
A cewarsa:
“Amma duk da haka, ban sauya addini ba, domin matsalar ’yan bindiga ta shafi kowa a Arewa, ina mai gode wa Allah da Musa ya gane kuskurensa.
Matan Musa sun bayyana cewa za su tsaya tare da shi domin ganin ya ci gaba da rayuwa a Sokoto kuma ya dawwama a kan tafarkin addinin Musulunci.
Malamin coci ya koma addinin gargajiya
Kun ji cewa tsohon malamin coci, Dr Echezona Obiagbaosogu, ya bayyana barinsa aikin coci domin rungumar addinin gargajiya.
Dr. Obiagbaosogu, wanda yake malami a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, ya yi bayani ne bayan gama rubutunsa na digirin-digirgir kan maganin gargajiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng