An yi sulhu tsakanin Bafarawa da Wamakko

An yi sulhu tsakanin Bafarawa da Wamakko

Ƴan siyasar Sokoto da ke gaba da juna, tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun sassanta bayan wata musayar kalamai da suka yi a bainar jama'a.

Jiga-jigan ƴan siyasar biyu sun haɗu ne wurin ta'aziyar malamin addinin musulunci Abbas Babi da ya rasu ranar Talata a Sokoto.

Daily Trust ta ruwaito cewa Wamakko ne ya fara isa gidan gaisuwar sannan bayan ƴan mintuna Bafarawa da magoya bayansa suka iso.

Bafarawa da Wamakko sun hadu watanni bayan musayar kalamai a filin jirgi
Bafarawa da Wamakko sun hadu watanni bayan musayar kalamai a filin jirgi. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Wamakko ya bukaci Bafarawa ya mika gaisuwar ga iyalan mamacin a madadinsu amma Bafarawa ya ce sai dai Wamakkon ya wakilce su kuma hakan aka yi.

Bayan sun gama ta'aziyar, Wamakko ya yi wa Bafarawa rakiya zuwa motarsa kuma suna tattauna na tsawon mintuna kafin suka rabu.

DUBA WANNAN: Wata mata ta ce tana da asirin amshe kudaden attajirai

"Mun yi farin ciki da wannan cigaban da aka samu.

"Wannan lamari ne da bai cika faruwa ba saboda sun daɗe ba su shiri da juna," a cewar wani magoyin bayan su.

A watan Disambar 2019 ne yan siyasar biyu suka yi cacar-baki a filin tashin jirage na Sultan Abubakar III da ke Sokoto.

Ran Bafarawa ta ɓaci ne bayan da magajinsa, Wamakko ya kira shi ɗan ci rani a Sokoto hakan yasa ya ƙi amsa gaisuwar sa a filin jirgin.

"Kai da ka kira ni ɗan ci rani a Sokoto, wacce gaisuwa kuma za ka yi min?.

"Mahaifi na da kakanni na ɗuk haifaffun Sokoto ne kuma zan iya nuna maka ƙaburburansu.

"Shin kai za ka iya nuna mana kabarin kakan ka?," Kamar yadda rahotanni suka ruwaito Bafarawa ya na cewa.

Daga bisani dai jirgi ɗaya suka hau zuwa birnin tarayya Abuja bayan wannan musayar kalaman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164