Nigerian news All categories All tags
Ridda: Matashi ya bar addinin Musulunci, ya koma Kirista

Ridda: Matashi ya bar addinin Musulunci, ya koma Kirista

Wani matashi, Baba Sabana Afcort, a jihar Adamawa ya bar addinin musulunci tare da komawa addinin kirista.

Jaridar Rariya ta rawaito cewar matashin abokin gwagwarmayar ne a dandalin sada zumunta.

Jaridar ta kara da cewar, bayan samun rahoton abinda matashin ya aikata, sun kira shi kuma ya tabbatar da masu cewar labarin gaskiya ce.

Ridda: Matashi ya bar addinin Musulunci, ya koma Kirista

Ridda: Matashi ya bar addinin Musulunci, ya koma Kirista

Labarin riddar Baba Sabana ta jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta a inda wasu ke nuna takaicinsu wasu kuma ke ganin dama hakan ba wani abun mamaki bane musamman idan aka yi la'akari da sunan matashin.

DUBA WANNAN: Dumu-dumu: An kama wasu matasa suna sata a wani gida a Kano, duba hotunansu

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar, wani yaro mai shekaru 13 kuma da ga wani jami'in dan sanda ya rataye kansa, kamar yadda hukumar ta sanar a yau.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Gombe, DSP Mary Malum, ta bayyana cewar an samu gawar yaron, Muhammadu Al-amin, rataye a dakinsa.

Malum ta ce, a ranar Litinin da misalin karfe 4:00 na yamma, mahaifin yaron, Inspekta Abdu Manu dake aiki da sashen binciken laifuka a ofishin 'yan sanda dake Pantami, ya samu kiran waya daga matar sa cewar an samu dansu mai shekaru 13 ya rataye kansa a dakinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel