An Rasa Rayuka 2, Wasu 22 Sun Raunata a Turmutsutsun Filin Idi, Gwamna Ya Yi Bajinta
- Rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon turmutsutsu da ya auku a babban filin Sallar idi na Gombe a ranar Lahadi
- Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na safe yayin da jama’a suka yi kokarin fita cikin gaggawa, lamarin da ya janyo jikkatar mutum 22
- An garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban, yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ya dauki nauyin jinyar dukkan wadanda suka sami raunuka
- Rundunar ‘yan sanda ta jajanta wa iyalan wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon turmutsutsu a sallar idi.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a babban filin Sallar idi na Gombe a ranar Lahadi 30 ga watan Maris din shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

Asali: Facebook
An rasa rayuka a cunkoson filin idi
Hakan na cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar ga ƴan jaridu, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma sauran wasu da suka samu raunuka.
Buhari Abdullahi ya ce:
“Hukumar ‘yan sandan Gombe na son sanar da jama’a game da hadarin turmutsutsu da ya faru a babban filin Sallar idi na Gombe.
“Abin takaici, likita ya tabbatar da mutuwar Aisha Salisu Ahmed mai shekara 4 da rabi da Maryam Abdullahi Gwani mai shekara 4.
“Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 30/03/2025, da misalin karfe 10:45 na safe, a kofar fita daga filin Sallar idi, bayan an kammala salla.
“Gagarumin taron jama’a, musamman mata da yara, sun yi kokarin fita cikin gaggawa, wanda hadin tsananin zafi ya haddasa turmutsutsu, inda mutum 22 suka jikkata.”
An yi gaggawar kai dauki, inda motocin asibiti daga gidan gwamnatin Gombe suka kai mutum 15 asibitin Zainab Bulkachuwa, an kai sauran bakwai Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH).

Kara karanta wannan
An farmaki ƴan Hisbah yayin hana ƙwallo a masallacin da ake tahajjud, sun samu raunuka

Asali: Facebook
Gwamna ya dauki nauyin majinyata a Gombe
Daga bisani, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya nuna damuwa kan lamarin inda ya dauki nauyin jinyar wadanda suka jikkata.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya dauki nauyin biyan kudin jinyar duk wadanda suka jikkata.”
Rundunar ‘yan sanda ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata kuma ke karbar magani.
Legit Hausa ta yi magana da wani
Wani da ya halarci salla a masallacin, Alkasim Muhammad Isa ya ce tabbas an samu hatsaniya wanda mutane da yawa sun jikkata.
Ya ce:
"An ce wasu sun mutu amma ban san mutum nawa ba ne, an kai wasu asibitin Zainab Bulkachuwa da ke kusa da wurin."
Alkasim ya ce abin bai yi dadi ba duba da yadda ana cikin farin cikin bukukuwan sallah amma lamari ya zo da haka.
Seyi Tinubu: An daka wawa a motar abinci
Kun ji cewa wasu matasa sun farwa motar abinci da ake zargin ta ɗauko tallafin da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu zai rabawa jama'a a jihar Gimbe
Majiyoyi sun bayyana cewa matasan sun dakawa motar wawa, suka kwashe kayan da suka haɗa da shinƙafa, sukari da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng