Ana Shirin Fara Duban Watan Sallah, Sarkin Musulmi Ya Gwangwaje Matasa 2 da Kyauta Mai Tsoka
- Matasa 2 daga cikin masu yi wa kasa hidima (NYSC) a jihar Sakkwato sun lashe lambar yabon fadar Sarkin musulmi da gwamnatin jiha
- Fadar sarkin musulmi ta ba kowane ɗaya daga cikinsu kyautar talabijin na sa wa a bango da kuma N100,000 saboda kyawawan halayensu
- Shugaban NYSC na Sakkwato, Alhaji Usman Yakubu Yaro ya ce yana fatan wasu matasa daga jihar su ci kyautar shugaban ƙasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Wasu ‘yan bautar ƙasa guda biyu na rukunin 'Batch A Stream 2' da aka tura jihar Sakkwato sun samu lambar yabo daga fadar mai alfarma sarkin musulmi.
Fadar Sultan da Gwamnatin Jihar Sakkwato sun gwangwaje matasan da kyauta mai tsoka saboda kyakkyawan halayensu da sadaukarwarsu a lokacin bautar ƙasa.

Asali: Facebook
A rahoton Leadership, Fadar Sultan ƙarƙashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ta ba wa namiji da mace, ƴan NYSC kyaututtuka biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fadar basaraken ta ba matasan da suka fi nuna halaye masu kyau kyautar talabijin na jikin bango (Plasma TV) da kuma N100,000 kowannensu.
Me yasa sarkin Musulmi ya ba su kyauta?
Kodinetan NYSC na jihar Sakkwato, Alhaji Usman Yakubu Yaro, ya bayyana cewa an bada wannan lambar yabo mai ƙunshe da kyautuka ne domin ƙarfafa wa matasam gwiwa su zauna su yi hidima a yankunan karkara.
A cewarsa, yawancin ‘yan NYSC su na ƙauracewa yankunan karkara, bisa haka aka tsara wannan lambar yabo domin jawo hankalinsu su zauna su yi aiki a wuraren da ake buƙatarsu sosai.
Kodinetan ya kuma yi fatan cewa wasu daga cikin matasa ma su yi wa ƙasa hidima daga jihar Sakkwato za su samu lambar yabo ta Shugaban Ƙasa.
Yadda ake ba ƴan NYSC horon sana'o'i
Usman Yakubu ya bayyana cewa NYSC ta haɗa gwiwa da wasu hukumomi domin koyar da matasa sana’o’i, don ba su damar zama masu dogaro da kansu bayan gama hidima ga ƙasa.

Kara karanta wannan
Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a
Har ila yau, ya gargadi waɗanda suka yi kuskure a lokacin yi wa kasa hidima cewa za a hukunta su, domin NYSC shiri ne da ke bayar da lada ga nagari kuma ya na hukunta masu laifi.

Asali: UGC
Daga ƙarshe, kodinetan NYSC na Sakkwato ya shawarci matasan ƴan bautar ƙasa da su zauna lafiya, su kasance jakadu nagari a duk inda suka tsinci kansu
Bugu da ƙari, ya buƙaci matasan da su guji tafiye-tafiye da daddare domin kare lafiyarsu daga faɗawa sharrin matsalar tsaron da ake fama da ita.
An shanya ƴan NYSC a tsakar rana
A wani labarin, kun ji cewa sojojin da ke ba matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Kano sun shanya wasu matasa a tsakar rana, lamarin da ya jawo raddin jama'a.
A cikin bidiyo da ake ta yada wa a kafar Instagram, ya nuna lokacin da wasu 'yan NYSC ke barci a tsakar rana, wasu kuwa sun dauki abin wasu suna ci gaba da annushuwarsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng