Bidiyon yadda aka shanya 'yan NYSC a Kano su kwanta a rana saboda wani laifi

Bidiyon yadda aka shanya 'yan NYSC a Kano su kwanta a rana saboda wani laifi

  • 'Yan bautar kasa sun gamu da fushin sojojin da ke koya musu fareti a sansanin bautar kasa ta jihar Kano
  • An gano wani bidiyo lokacin da wasu 'yan bautar kasa a Kano ke shanye a rana bisa laifin kin halartar filin fareti
  • Mutane da dama a kafar Instagram sun yi martani, inda kowa ya bayyana ra'ayinsa kan wannan lamari

Kano - Mutane da dama sunyi martani biyo bayan ganin wani bidiyo na membobin bautar kasa na NYSC da aka tilastawa bacci cikin zafin rana.

Legit.ng ta tattaro cewa an yi wa yan bautar kasa da ke zama a sansanin NYSC ta jihar Kano wannan hukuncin ne bisa laifin kin halartar filin fareti.

A cikin bidiyon da Instablog9ja ya yada a kafar Instagram, ya nuna lokacin da wasu 'yan NYSC ke bacci a tsakar rana, wasu kuwa sun dauki abin wasu suna ci gaba da annushuwarsu.

Kara karanta wannan

Dalibin da ke zuwa makaranta a kan keke duk ruwa duk iska ya samu tallafin mutumin kirki

Bidiyon yadda aka tilasta 'yan NYSC a Kano su kwanta rana saboda wani laifi
'Yan NYSC shanye a rana a Kano | Hoto: Instablog9ja
Asali: UGC

'Yan bautar kasa sun kwanta a rana a kan katifunsu, alamu sun nuna an hukunta 'yan bautar kasan ne.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a a kafar Instagram

@koko_son_of_a_gun ya yi martani da cewa:

"Lmfaooooooooo. Na yi zaman sansani a Kano na shirin NYSC. Daga karaye junction zuwa sansanin da kanta babu wanda ya iya turanci sai mutum daya da ya sayar min bokiti. Direban da ya kaini garin Kano bai iya magana da turanci ba shi ma."

@sandie_bgfl ya ce:

"Wannan mutumin da ya kwanta sakaka tare da shimfida kafafunsa ya bani dariya."

@daisyijay ya ce:

"Omo, kwanakin nan ina karkashin gado nake buya, babu yadda sojojin za su gan ni"

@timz_0 yayi sharhi:

"Idan na dauko mayafi na lullube jikina ko,,, zance ya kare ,,, su da kansu za su zo su ce na tashi."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

@keshacosmetics opined:

"A nan ne na yi zaman sansanin bautar kasa, wahalar ba daga nan take ba, daga harbe-harbe, zuwa tsananin zafi, da safiya mai tsananin sanyi da tsoron macizai"

'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

A wani labarin, 'Yan sandan New Zealand sun kama wasu mutane biyu da ke kokarin shigo da mota da ke cike da soyayyun kaji zuwa Auckland, The Punch ta ruwaito.

Auckland, birni mafi girma a kasar, yana cikin tsauraran ka'idojin takunkumi na Korona tun tsakiyar watan Agusta, ba tare da an ba kowa izinin shiga ko barin yankin ba.

Duk kasuwancin da ba su da mahimmanci, wanda ya hada da wuraren cin abinci na kan titi, an rufe su a Auckland. Sai dai, sauran yankunan New Zealand na da karancin ka'idoji tare da kusan dukkanin nau'ikan kasuwanci a bude.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel