Fashewar Tankar Mai: Yadda Mutane 112 Suka Mutu garin Kwasar Fetur a Jihar Neja

Fashewar Tankar Mai: Yadda Mutane 112 Suka Mutu garin Kwasar Fetur a Jihar Neja

  • A jihar Neja, fashewar tankokin mai sun hallaka mutane 112 tare da lalata kadarorin biliyoyin Naira daga Janairu zuwa Maris 2025
  • Ranar 18 ga Janairu, wata tankar mai dauke da lita 60,000 ta fashe a kwanar Dikko, kan hanyar Abuja-Kaduna, mutane 105 suka mutu
  • A cikin Maris kadai, an samu fashewar tankokin fetur uku a yankuna daban-daban, yayin da aka samu uku a Janairu da daya a Fabrairu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Fashewar tankunan mai a Jihar Neja sun hallaka akalla mutane 112 tare da lalata kadarorin da darajarsu ta kai biliyoyin naira tsakanin Janairu da Maris 2025.

A cikin watanni ukun da suka gabata, bayanan da aka tattara sun nuna cewa hadurran tankuna bakwai sun jikkata mutane da dama tare da haddasa asarar dukiya.

Kara karanta wannan

'Yara miliyan 1.5 za su mutu': Najeriya na fuskantar sabuwar barazana daga Amurka

Rahotanni sun bayyana yadda mutane 112 suka mutu a fashewar tankokin mai a Neja
Rahoto: Fashewar tankokin mai a Neja ya jawo asarar rayukan mutane 112. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A watan Maris kadai, an samu fashewar tankuna uku a jihar Neja, yayin da aka samu fashewa daya a watan Fabrairu da kuma uku a Janairu, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Neja: Hatsarin tankar mai mafi muni a Janairu

Bincike ya nuna cewa, a ranar 18 ga Janairu, 2025, an samu fashewar tankar mai mafi muni a kwanar Dikko, kan hanyar Abuja-Kaduna, wata tanka mai dauke da lita 60,000 na fetur ta fashe, ta kashe mutane 105.

Lamarin ya bar wasu da raunuka, sannan ya haddasa asarar kadarori da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.

Rahotanni sun nuna cewa, lokacin da tankar ta yi hatsari, jikinta ya rabu da kanta, wanda hakan ya sa ta fadi ta zubar da fetur.

Ganin man fetur na zuba malala a kasa, ya sa mutane da dama suka taru a wajen suna kwasar man. Sai dai, kafin a ankara, wuta ta tashi, tare da haddasa fashewar tankar, da ta cinye yankin baki daya.

Kara karanta wannan

Masu bautar kasa a Najeriya na cikin alheri dumu dumu, Tinubu ya fara biyan N77, 000

Sai dai wannan ba shi ne karshen hatsura irin wannan ba, domin daga Janairu zuwa Maris, an samu wasu fashewar tankuna daban-daban a jihar.

Karin hadurran tankar mai a jihar Neja

Bayan kwanaki biyu da fashewar tankar mai a Dikko, a ranar 20 ga Janairu, wata tankar mai ta fadi kuma ta fashe a kusa da Lapai, kan hanyar Lapai-Agaie.

A cewar mazauna yankin, tankar ta yi karo da wata motar dakon kaya da ke tsaye a gefen hanya, lamarin da ya haddasa gobara. Sai dai, babu asarar rai a wannan hatsarin.

Haka nan, a ranar 27 ga Janairu, wata tankar mai ta sake faduwa kuma ta fashe a Kusogbogi, wani kauye da ke kusa da Lapai, akan hanyar Lapai-Agaie.

Babu wanda ya rasa ransa, amma fashewar ta jefa jama’a cikin firgici tare da haddasa asarar fetur da kudinsa ya kai miliyoyin naira.

Bincike ya kuma gano cewa, a ranar 8 ga Fabrairu, wata tankar gas ta fashe a Sabon-Wuse, karamar hukumar Tafa, yayin da ake juye wa wata tanka gas a tashar mai.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya sanar da rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Baba Karkuzu

Duk da cewa babu asarar rai, gobarar ta lalata kadarori, ciki har da mota daya da buhunan farin wake da waken soya sama da 550.

Tankokin mai sun fashe sau 3 a Maris

Hukumar NSEMA ta yi magana kan fashewar tankokin mai da suka afku a jihar Neja
An samu fashewar tankokin man fetur sau uku a Maris, yayin da NSEMA ta yi karin bayani. Hoto: @nemanigeria
Asali: Twitter

A watan Maris, an samu fashewar tankuna uku a jihar Neja. Fashewar farko ta faru ne a ranar 4 ga Maris a Karamin-Ramin, karamar hukumar Mashegu, inda mutane bakwai suka mutu.

Haka kuma, a ranar 23 ga Maris, an samu fashewar tankuna biyu a lokaci daban; daya a tashar mai ta AA Rano a Kontagora, dayar kuma a kan hanyar Badeggi-Agaie.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta bayyana fashewar tankar mai a ranar 18 ga Janairu a matsayin mafi muni a 'yan shekarun nan.

Haka kuma, hukumar ta tuno da wata fashewa da ta kashe mutane 58 a watan Satumbar 2024.

A cewar Dr Ibrahim Audu Hussaini, daraktan yada labarai da ayyukan musamman na NSEMA, fashewar ranar 8 ga Satumba, 2024, ta faru ne a kan hanyar Agaie-Bida, kusa da kauyen Man-Woro, lokacin da wata tankar mai dauke da fetur ta kife, ta zubar da man, sannan ta kama da wuta.

Kara karanta wannan

Wani abin fashewa ya tarwatse a cibiyar haƙo mai a Rivers bayan dakatar da Fubara

Gobara ta cinye wata motar dakon shanu da mutane a cikinta, da wata motar bas mai dauke da fasinjoji.

Rahotanni sun nuna cewa motar daukar shanu ta taso ne daga Wudil, Jihar Kano, tana kan hanyarta zuwa Legas, yayin da motar bas din ke kan hanyarta zuwa kasuwar Agaie.

Tankar man fetur ta fashe a Taraba

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ranar Laraba, 22 ga Janairu, 2025, wasu matasa sun taru a wurin da wata tankar mai ta yi hatsari a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Jami’an NSCDC da ‘yan sanda sun dakatar da matasan a yankin Mile 6 da ke Jalingo, inda tankar ta kife ta zubar da mai, domin hana aukuwar irin hadarin da ya faru a Neja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng