Musulmin Najeriya Sun Yi Babban Rashi, Sheikh Muhammad Ya Rasu ana Shirin Sallah

Musulmin Najeriya Sun Yi Babban Rashi, Sheikh Muhammad Ya Rasu ana Shirin Sallah

  • Allah ya yi wa shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar JIBWIS watau Izala reshen jihar Yobe, Imam Muhammad Khuludu Geidam rasuwa
  • Kungiyar Izala ta bayyana cewa malamin ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba, 26 ga watan Ramadan, 1446AH daidai da 26 ga watan Maris, 2025
  • Malamin ya ba da gudummuwa sosai ga al'umma ta fuskar wa'azi da ilimantar da jama'a hanyar rayuwa mai inganci bisa koyarwar addinin musulunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen jihar Yobe, Sheikh Imam Muhammad Khuludu Geidam ya rasu.

Fitaccen malamin addinin musuluncin ya riga mu gidan gaskiya ne yau Laraba, 26 ga watan Maris, 2025 daidai da 26 ga watan Ramadan, 1446AH.

Sheikh Muhammad Khuludu Geidam.
Allah ya yi wa Sheikh Muhammad Khuludu Geidam rasuwa Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Ƙungiyar Izala ta Najeriya ce ta sanar da rasuwar shugaban Majalisar malamai na Yobe a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Babban malami ya hango matsala a Kano, an nemi alfarmar sarki kan hawan Sallah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi jana'izar Sheikh Muhammad Khuludu Geidam

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an tsara yi masa jana’izar a yau Laraba da misalin karfe 5:30 na yamma a garin Geidam da ke jihar Yobe a Arewa maso Gabas.

Sheikh Imam Muhammad Khuludu Geidam fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ya yi hidima mai yawa ga al’umma, musamman a fannin wa’azi da karantar da ilimin addini.

A matsayinsa na shugaban Majalisar Malamai na Jibwis a Yobe, ya taka rawar gani wajen yaɗa tauhidi da kuma ilmantar da jama’a kan hanyoyin inganta rayuwa bisa koyarwar Musulunci.

Musulmin Najeriya sun yi babban rashi

Mutuwarsa ba ƙaramar rashi ba ce ga al’ummar Musulmin Najeriya musamman mabiya ƙungiyar Izala, waɗanda a yanzu suka fara jimami da alhinin rasuwar jagora nagari.

Makusantan marigayin sun bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga addini da al’umma.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

Bayan sanar da rasuwar, malamai da jama’a daga sassa daban-daban na kasar nan sun fara aika sakonnin ta’aziyya ga iyalai, dalibai da kuma daukacin al’ummar Yobe.

Ana sa ran manyan malamai, shugabanni da dubban Musulmi za su halarci jana’izar malamin a Geidam domin yi masa addu’a da rokon Allah Ya jikansa da rahama.

Malamin ya ba da gudummuwa ga Musulunci

An bayyana marigayin a matsayin jigo wanda Allah ya yi wa baiwa da ilimi da kishin Musulunci, kuma koyarwarsa ta taimaka matuka wajen ilmantar da jama’a a fadin jihar da ma Najeriya baki daya.

Allah Ya jikan Sheikh Imam Muhammad Khuludu Geidam, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya aljanna ce makomarsa. Amin.

Babban malami a ƙasar Masar ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa an shiga jimami a ƙasar Masar da Allah ya karɓi rayuwar malamin addinin Musulunci, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini, a ranar Litinin.

An tattaro cewa marigayin ya yi fice a fannin karantar da Hadisan Manzon Allah SAW da koyar da sunnoninsa, kuma yana daga cikin manyan malaman Salafiyya a Masar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng