Maganar Kirkirar Sababbin Jihohi Ta Dawo, Kudirin Ya Tsallake Karatu na 2 a Majalisa

Maganar Kirkirar Sababbin Jihohi Ta Dawo, Kudirin Ya Tsallake Karatu na 2 a Majalisa

  • Majalisar Wakilai ta amince da karatu na biyu na kudirori hudu da ke neman kirkirar sababbin jihohi a Najeriya
  • Bugu da kari, an amince da wasu karin kudirori 38 da ke neman sauya kundin tsarin mulki na shekarar 1999
  • Sababbin jihohin da ake so a kirkira su ne Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga, Orlu da Etiti domin hadewa da jihohi 36
  • Bayan kada kuri’a a zaman Majalisa, an tura kudirorin zuwa kwamitin da ke duba gyaran kundin tsarin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai a birnin Abuja ta yi zama kan kudirin ƙirƙirar sababbin jihohi a Najeriya.

Majalisar ta amince da karatu na biyu na kudirori hudu da ke neman kirkirar karin jihohi a fadin kasar nan.

Majalisa ta yi zama kan kudirin ƙirƙirar sababbin jihohi
Kudirin kirkirar sababbin jihohi a majalisa ya tsallake karatu na 2. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Cibiya ta hango yaudara wajen kirkirar jihohi

Kara karanta wannan

2027: 'Yan majalisa na kwaskware tsarin zaben shugaban kasa da gwamnoni

Haka kuma, Majalisar ta amince da wasu kudirori 38 da ke neman sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 a kokarin da ake na gyaransa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wata cibiya ta zargi APC da kawo maganar kirkirar sababbin jihohi domin shirin makarkashiya kan zaben 2027.

Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam (CHRICED) ta zargi jam'iyyar APC da amfani da shirin kirkirar jihohi don yaudarar 'yan Najeriya kafin zaben 2027.

Shugaban CHRICED, Ibrahim Zikirullahi, ya ce APC na amfani da shirin a matsayin tarko don samun goyon baya duk da sanin rashin yiwuwar hakan.

Zikirullahi ya gargadi cewa kirkirar sababbin jihohi zai kara tsananta matsalar tattalin arziki, inda yawancin jihohi ke fama da rashin biyan albashin ma’aikata.

Majalisa ta tabbatar da kudirin ƙirƙirar sababbin jihohi
Kudirin kirkirar sababbin jihohi a a majalisar wakilai ya tsallake karatu na 2. Hoto: Hon. Tajudden Abbas.
Asali: Facebook

Sauran kudurori da aka duba a majalisa

Kudirorin guda 42 da aka tsara su bisa sassa daban-daban sun tsallake karatu na biyu ne bayan gabatar da su a zaman Majalisa da Hon. Julius Ihonvre ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

Daga cikin kudirorin akwai wanda ke neman samar da jihohin Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga, Orlu da Etiti, wanda 'yan Majalisa daban-daban suka dauki nauyin gabatarwa.

Bayan kammala karanta su, mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ya kada kuri’a kan kudirorin, inda suka tsallake karatu na biyu.

Daga nan aka tura su zuwa kwamitin Majalisa na gyaran kundin tsarin mulki karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, cewar The Nation.

A baya, Majalisar ta amince da wasu kudirori 39 na gyaran kundin tsarin mulki, su ma aka tura su zuwa kwamitin domin ci gaba da aiki a kansu.

Duk yadda aka kare, shugaban kasa ne yake da ta-cewa wajen na'am ko watsi da kudirin.

An gabatar da kudirin sababbin jihohi 31

Kun ji cewa Kwamitin Majalisar Wakilai kan duba kundin tsarin mulki ya ce an gabatar da bukatun kirkiro sabbin jihohi 31 daga yankuna shida na Najeriya.

Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ya karanta wasikar da ke bayyana sharuddan da dole ne a cika kafin a amince da kirkiro jihohi.

Wasikar ta ce sashe na 8 na kundin tsarin mulki ya tanadi bukatun da dole ne a bi, ciki har da amincewar kashi uku na 'yan majalisa kafin kafa jiha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng