An Shiga Firgici a Jami'ar Sokoto, Gobara Ta Tashi a Dakin Kwanan Dalibai Mata

An Shiga Firgici a Jami'ar Sokoto, Gobara Ta Tashi a Dakin Kwanan Dalibai Mata

  • Gobara ta tashi a sabon ɗakin kwanan dalibai mata na jami’ar jihar Sokoto (SSU), lamarin da ya jefa mutanen da ke cikin jami’ar cikin firgici
  • An ce gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga Maris, ta lalata sabon ginin da aka kammala kwanan nan
  • Wata daliba da ta zanta da Legit.ng ta bayyana cewa babu dalibai a cikin ginin lokacin da gobarar ta tashi, domin an sauya musu wurin zama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Mummunar gobara ta tashi a sabon ɗakin kwanan dalibai mata a jami’ar jihar Sokoto (SSU), lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Maris, inda gobarar ta babbake sabon ginin.

Kara karanta wannan

Natasha: Fada ya barke a majalisa, an yi kaca kaca tsakanin sanata da tsohuwar minista

Dalibai sun yi magana da sabon ginin dakin kwanan dalibai mata ya kama da wuta a jami'ar Sokoto
An tabbatar da konewar sabon dakin kwanan dalibai mata a jami'ar Sokoto. Hoto: Stringer
Asali: Getty Images

Sokoto: Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai

Rahoton Legit.ng ya nuna cewa ɗakin kwanan da gobarar ta shafa yana cikin sababbin gine-gine da aka gina domin magance matsalar wurin kwanan dalibai a jami’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, kamar yadda wata daliba ta shaidawa Legit.ng cewa "har yanzu ba a san abin da ya jawo tashin wutar ba."

Dalibar ta bayyana cewa babu wani dalibi da ke zaune a cikin ɗakin kwanan a lokacin da gobarar ta tashi, saboda wani umarni da jami’ar ta bayar.

A cewar dalibar da ta zanta da wakilinmu:

"An riga an sallami daliban da ke zaune a wannan sabon ɗakin kwanan, inda aka mayar da su tsohon ɗakin kwana. Mahukuntan makarantar ne kawai suka san dalilin daukar matakin."

Ba a tatance barnar da gobarar ta yi ba

Shugaban ɗalibai a jami’ar ya tabbatar da cewa jami’an kashe gobara sun isa wurin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma domin dakile wutar.

Kara karanta wannan

An hango alkalin da ya jika wa Fubara aiki a Rivers zaune da Wike, kotu ta yi bayani

A yayin da 'yan kwana kwana suka yi kokarin kashe wutar, ba a kai ga tantance girman asarar da aka tafka ba har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto.

Sabon ɗakin kwanan yana cikin wani shirin gwamnati na samar na karin masaukai ga ɗaliban jami’ar domin rage cunkoso da matsalar rashin wurin kwana.

A cikin ‘yan shekarun nan, jami’ar na fama da ƙarancin ɗakunan kwana, wanda ke tilasta wa ɗalibai da dama neman dakunan kwana a waje.

Dalibai da mahukunta na murnar kammala gina sabon dakin kwanan daliban, da tunanin zai taimaka wajen shawo kan matsalar rashin wurin kwana, kafin afkuwar wannan gobara.

Takaitaccen bayani kan jami'ar jihar Sokoto

Rahotanni sun yi bayani kan gobarar da ta tashi a jami'ar jihar Sokoto
Dalibai maza da mata a harabar jami'ar jihar Sokoto (SSU). Hoto: @ssu_exclusive
Asali: UGC

Bayanai daga shafin Wikipedia ya nuna cewa an kafa jami’ar jihar Sokoto (SSU) a shekarar 2009, kuma an ƙaddamar da matsugunnin jami’ar a ranar 29 ga Oktoba, 2013.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: INEC ta karbi bukatar yi wa Sanata Natasha kiranye daga majalisa

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ne ya ƙaddamar da jami’ar a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Alhaji (Dr) Aliyu Magatakarda Wamakko.

Tsohon shugaban jami’ar, Farfesa Nuhu O. Yaqub, OFR, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an tabbatar da ci gaban jami’ar, har zuwa lokacin saukarsa.

A halin yanzu, jami’ar jihar Sokoto na gudanar da akalla shirye-shiryen karatu guda 62 a cikin manyan bangarori biyar.

ASUU ta shiga yajin aiki a jami'ar Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ASUU reshen Jami’ar Jihar Sokoto ta tsunduma yajin aiki na sai baba ta gani, bisa rashin magance matsalolin da ke addabar ta.

Kungiyar ta bayyana cewa yajin aikin zai dakatar da dukkan harkokin jami’a, ciki har da koyarwa, jarrabawa, da tantance sakamakon dalibai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng