'Bai Gajiya a Gado': Mata a Kaduna Ta Nemi Saki, Ta Fadi Faman da Take Yi da Jima'i

'Bai Gajiya a Gado': Mata a Kaduna Ta Nemi Saki, Ta Fadi Faman da Take Yi da Jima'i

  • Wata matar aure mai shekara 37 a Kaduna ta nemi kotu ta raba aurensu saboda yawan bukatar kwanciya da mijinta ke yi da ita kowace rana
  • Linda Stephen ta bayyana cewa mijinta, Felix, ya na yi mata duka idan ta ki amincewa da bukatarsa, duk da cewa sun shafe shekaru shida tare
  • Ta ce ya kan tare da ita daga tsakiyar dare har safiya, kuma duk da kukan da take yi, baya dakatawa
  • Mijin nata, Felix, ya roki kotu da ka da ta raba aurensu, yana mai cewa yana ƙaunar matarsa, kuma yanzu ya shirya rage bukatar saduwar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wata matar aure, Linda Stephen, ta nemi kotun majistare a Kaduna da ta raba aurensu a Kaduna.

Matar auren mai shekara 37 ta roki kotun ne saboda yawan bukatar jima'i daga mijinta mai suna Felix Stephen.

Kara karanta wannan

'Za ku iya halaka nan take': Fitaccen Sarki ya gargadi masu neman tuge shi a sarauta

Mata ta koka da yawan bukatar jima'i da mijinta ke da shi
Matar aure a Kaduna ta roki kotu ta raba aurensu da mijinta saboda jarabarsa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mata ta nemi saki a kotu saboda jaraba

A cikin roƙonta, Linda, da ke zaune a Unguwan Sunday, ta ce mijinta yana dukanta idan ta ki amincewa da bukatar kwanciyarsa a cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta tabbatar da irin cin zarafin da yake yi mata idan ta ki amincewa da bukatunsa duk da sun shafe shekaru shida tare da aure.

Ta shaida wa kotu cewa ba ta da sha’awar ci gaba da zama da mijinta saboda ba za ta iya jure masa ba.

Ta ce:

"Ina rokon kotu ta raba auren nan saboda ba zan iya jure wannan bukata tasa ba, yana son jima’i da yawa, kuma ba zan iya jurewa ba.
"A mafi yawan lokuta, ya na yi daga tsakiyar dare har safiya, ko da ina kuka, ba ya dakatawa.
"Yanzu haka watanni uku kenan da na bar gidansa, yan uwansa suna rokon na koma, amma ba su san halin da nake ciki ba."

Kara karanta wannan

Ramadan 2025: Ana tafka tsananin zafin rana a Kano, masu azumi sun koma shan ORS

Mata ta nemi saki a kotu kan jarabar mijinta a Kaduna
Matar aure ta bukaci saki a kotu kan yawan buƙatar jima'i da mijinta ke yi. Hoto: Getty Images. (An yi amfani da hoton ne kawai domin misali, bai da alaka da labarin.
Asali: UGC

"Zan rage sha’awata" – cewar mijin

Matar ta kara da cewa mijinta baya iya daidaita sha’awarsa, kuma idan ta ki amincewa da bukatarsa, yana dukanta ko a gaban ‘ya’yansu biyu.

A martaninsa, Felix Stephen ya shaida wa kotu cewa yana ƙaunar matarsa, kuma bai son a raba aurensu.

Ya roki kotu da ta lallasheta don ta zauna da shi, yana mai cewa yanzu ya shirya rage bukatar jima’insa, Daily Post ta ruwaito.

Ya ce:

"Na tafi da kawuna da abokaina zuwa gidan iyayenta don roƙonta, amma ta ƙi sauraronmu, maimakon haka, ta fice daga wurin."

Ya kara rokon kotu da ta ba shi lokaci don ya sasanta da matarsa kuma su daidaita tsakaninsu.

Alkalin kotun, John Dauda, ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Mayun 2025 don jin halin da suka tsinci kansu a ciki, sannan ya bukaci su ci gaba da zaman lafiya.

Jaruma Malika ta shiga kotu da mijinta

Kara karanta wannan

Pantami ya magantu bayan Aminu Ado da Sanusi II sun sanar da lokutan idi a Kano

A baya, mun ba ku labarin cewa wata jarumar Kannywood ta sake komawa kotu a Kaduna domin neman saki daga mijinta.

Jarumar Kannywood, Maryam Malika, ta roki kotun Shari’a da ke Magajin Gari a Kaduna, ta tabbatar da sakin da tsohon mijinta, Umar ya yi mata a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng