An Fara Ƙoƙarin Jiƙawa Tinubu Aiki a Rivers, An Nemi Kotu Ta Kori Shugaban Riƙo

An Fara Ƙoƙarin Jiƙawa Tinubu Aiki a Rivers, An Nemi Kotu Ta Kori Shugaban Riƙo

  • Babbar kotun tarayya ta karɓi ƙarar da ke neman soke nadin Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaban rikon kwarya na jihar Rivers
  • Wanda ya shigar da ƙarar, Johnmary Jideobi, ya nemi kotu ta ayyana nadin a matsayin haramun tare da hana shugaban ƙasa yin hakan a kowace jiha
  • Johnmary wanda lauya ne mai zaman kansa, ya ce kundin tsarin mulki bai bai wa Shugaba Bola Tinubu damar dakatar da zababben gwamna ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta karɓi ƙarar da ke neman soke nadin Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaban riko na jihar Rivers.

A cikin ƙarar, an ambaci Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ake ƙara na daya, yayin da ministan shari’a da wasu jami’ai suka kasance cikin jerin wadanda ake ƙara.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Jerin gwamnonin da suka goyi bayan Tinubu a dakatar da Fubara

Lauya ya yi magana da ya shigar da Tinubu kara kotu kan dakatar da gwamnan Rivers
Lauya ya nemi kotu ta fatattaki shugaban riko da Tinubu ya nada a Rivers saboda saba doka. Hoto: @officialABAT, @SimFubaraKSC (X)
Asali: Facebook

Rikicin Rivers: Lauya ya maka Tinubu a kotu

Wani lauya, Johnmary Jideobi, ne ya shigar da ƙarar, yana mai neman kotu ta soke duk wasu matakai da Ibas ya ɗauka a matsayin shugaban riko, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya bukaci kotu ta hana Shugaba Tinubu ko wani jami’insa tsige ko dakatar da gwamna da mataimakinsa a kowace jiha ta Najeriya.

Ya kuma bukaci a hana shugaban kasa naɗa shugaban riko a kowace jiha a matsain madadin zababbun gwamnonin da al’umma suka zaɓa a sahihin zabe.

A cikin takardar ƙarar, Johnmary Jideobi ya bukaci kotu ta fayyace ko shugaban kasa na da ikon tsige gwamna ko mataimakinsa ko naɗa shugaban riko a wata jiha.

An nemi kotu ta kori shugaban rikon Rivers

Ya ce duba da kundin tsarin mulkin Najeriya, babu wata doka da ta ba shugaban kasa damar tsige zababbun gwamnonin jihohi a kowane yanayi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da aka nemi Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Benuwai

Wanda ya shigar da ƙarar ya bukaci kotu ta ayyana cewa dakatar da gwamnan Ribas da mataimakiyarsa da shugaban kasa ya yi ya saba wa kundin tsarin mulki.

Har ila yau, ya bukaci kotu ta soke naɗin Vice Admiral Ibokette Ibas a matsayin shugaban riko na jihar Rivers, bisa rashin ingancin nadinsa.

TV360 Nigeria ta rahoto cewa mai ƙarar ya kuma nemi kotu ta umarci Ibas da ya gaggauta barin gidan gwamnatin jihar Rivers, domin an yi naɗinsa ba bisa ka’ida ba.

'Tinubu ba shi da iko kan gwamnoni' - Jideobi

Lauya ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba Tinubu damar dakatar da zababben gwamna ba
An nemi kotu ta hana Tinubu dakatar da gwamna a jihohin Najeriya. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A cikin takardar da ya gabatar, mai ƙara ya ce shugaban kasa na da ikon ayyana dokar ta-ɓaci, amma ba shi da iko kan zababbun gwamnonin jihohi.

Ya ce ba a ambaci mukamin shugaban riko a kundin tsarin mulki ba, don haka nadin Vice Admiral Ibokette Ibas abu ne da ya saba wa doka.

Kara karanta wannan

Tankar mai ta sake fashewa a Neja, hukumomi sun tashi tsaye

Johnmary Jideobi ya jaddada cewa gwamnonin jihohi ba hurumin shugaban kasa ba ne, domin tsarin mulkin Najeriya ya dogara ne a kan rarrabuwar iko.

Dalilin lauya na yin karar gwamnatin Tinubu

Lauyan ya ce ya shigar da ƙarar ne domin kare kundin tsarin mulki da kuma tabbatar da cewa ana bin doka a shugabancin kasar Najeriya.

Ya nuna damuwa kan cewa idan ba a dakatar da irin wannan mataki ba, shugaban kasa na iya yin hakan a kowace jiha, lamarin da zai jawo rikici.

Ya bukaci kotu ta gaggauta yanke hukunci domin hana ci gaba da dakatar da gwamnonin jihohi ba bisa doka ba.

Har yanzu ba a sa ranar da za a fara sauraron ƙarar ba, amma ana sa ran kotu za ta yanke hukunci kan lamarin nan gaba kaɗan.

Ana so Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Osun

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Oyewale Adesiyan, ya bukaci a ayyana dokar ta-ɓaci a Osun saboda yawaitar rashin tsaro da rikicin siyasa a jihar.

Adesiyan ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulki domin tabbatar da doka da oda tare da maido da zaman lafiya a Osun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng