Bayan Caccakar Tinubu kan Rikicin Rivers, Jonathan Ya Samu babbar Lambar Yabon Duniya
- Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya lashe kyautar Sunhak Peace ta 2025 saboda rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya a Afirka
- Kwamitin Sunhak Peace ya bayyana cewa Jonathan ya zama shugaban Afirka na farko da ya lashe wannan kyauta, bayan Ban Ki Moon da Hun Sen
- Shugaban Bola Tinubu, ya taya Jonathan murna, yana cewa wannan karramawa ta kara tabbatar da kokarinsa na inganta tsarin dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya lashe kyautar Sunhak Peace Award ta 2025, wadda ke girmama shugabanni masu kokarin kawo zaman lafiya a duniya.
Ikechukwu Eze, mai bai wa Jonathan shawara na musamman, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Litinin.

Asali: Twitter
Jonathan ya samu lambar yabo ta Sunhak

Kara karanta wannan
'Za ku iya halaka nan take': Fitaccen Sarki ya gargadi masu neman tuge shi a sarauta
Hadimin tsohon shugaban kasar, ya ce za a karrama Jonathan da kyautar ne a birnin Seoul, kasar Koriya ta Kudu, a ranar 11 ga Afrilu, 2025, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa Jonathan ya zama shugaba na farko daga Afirka da ya lashe wannan kyauta, bayan Ban Ki Moon da Hun Sen.
A cewar Eze, kwamitin ba da lambar yabo ta Sunhak Peace Prize ya ce an karrama Jonathan ne saboda gudunmawarsa wajen wanzar da zaman lafiya da kare dimokuradiyya a Afirka.
Wadanda ake karramawa da kambun Sunhak
An yaba masa musamman saboda rawar da yake takawa a kungiyoyin zaman lafiya da yake shugabanta, irin su gidauniyar Goodluck Jonathan (GJF) da WAEF.
Kyautar Sunhak Peace na cikin kyautuka guda biyu da kwamitin ke bayarwa duk bayan shekaru biyu ga shugabanni da kungiyoyin da suka taka rawar gani.
A baya, wasu fitattun shugabanni da suka lashe Sunhak Peace sun hada da tsohon shugaban Senegal, Macky Sall, da shugaban AfDB, Dr Akinwumi Adesina.
Sunhak: Tinubu ya taya Jonathan murna
A daidai wannan gabar, shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya taya tsohon Shugaba Jonathan murna kan wannan babban nasara da ya samu.
Hakan na kunshe ne a ciki wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, kuma Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.
A cikin sanarwar, Tinubu ya yabawa Jonathan bisa sadaukarwarsa wajen fafutukar zaman lafiya da hadin kan al'umma, "abin da ya ba shi matsayi a idon duniya".
Shugaba Tinubu ya ce samun wannan kyauta wata shaida ce da ke nuna kokarin Jonathan wajen wanzar da zaman lafiya da kare dimokuradiyya a Afirka da ma duniya.
Tinubu ya tuno da sadaukarwar Jonathan a 2015

Asali: Facebook
Ya tuna da yadda Jonathan ya zama gwarzon dimokuradiyya bayan amince wa da sakamakon zaben 2015 da kuma mika mulki cikin lumana.
Tinubu ya ce wannan mataki na Jonathan ya karfafa dimokuradiyyar Najeriya, tare da nuna kwarewa a harkar siyasa da shugabanci.
Shugaban ya kuma gode wa kwamitin Sunhak Peace Prize saboda karrama mutanen da ke kokarin inganta rayuwar al’umma a duniya baki daya.
Jonathan ya soki ayyana dokar ta baci a Rivers
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi Allah-wadai da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.
Goodluck Jonathan ya soki dakatar da gwamnan Rivers, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar, ya na mai cewa wannan matakin na iya ɓata sunan Najeriya.
Asali: Legit.ng