Kungiyar AGPMPN za ta karrama tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Abuja

Kungiyar AGPMPN za ta karrama tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Abuja

  • Kungiyar AGPMPN ta shirya bikin cika shekara 100 da kafu wa a Najeriya
  • Likitocin za su karrama Goodluck Jonathan saboda kokarin da ya yi a baya
  • Iyke Odo ya ce za a ba wadanda suka taka rawar gani a kasar lambar yabo

Abuja - Kungiyar likitoci ta AGPMPN za ta karrama tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da sauran wadanda suka bunkasa harkar kiwon lafiya.

The Cable ta rahoto cewa wannan kungiya za ta ba Goodluck Jonathan, Dr. Kayode Fayemi, da Olusegun Mimiko lambar yabo na kokarin da su ka yi.

Sauran wadanda za a karrama a ranar 12 ga Agusta, sun hada da tsohon tauraron Super Eagles Nwankwo Kanu da tsohuwar uwargida, Maryam Abacha.

Shugaban AGPMPN na kasa, Iyke Odo, ya fitar da jawabi, yace za su tuna da wadanda suka rubuta sunansu da ruwan gwal wajen bunkasa sha’anin lafiya.

“Za a shirya tattauna wa kan yadda za a gyara harkar kiwon lafiya a karkashin jagorancin Sanata Ken Nnamani bayan bikin bada lambar yabon a ranar.”

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

Goodluck Jonathan da Kanu zasu samu lambar yabo

“Daga cikin wadanda za a ba kyauta akwai tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, saboda kokarin da ya yi wajen yaki da cutar Ebola a lokacinsa.”
“Tauraro Kanu Nwankwo, ya samu shiga sahun nan saboda aikin da ya yi na kafa gidauniyar Kanu Heart Foundation da ke yi wa yara aiki a zuciya kyauta.”

Kungiyar AGPMPN za ta karrama GEJ
Goodluck Jonathan a majalisar dinkin Duniya Hoto: www.gadebate.un.org/en/68/nigeria
Asali: UGC

Kungiyar AGPMPN ta yi shekara 100 da kafu wa

Jarida Vanguard ta rahoto cewa an shirya wannan ne domin ayi murnar cikar AGPMPN cika shekara 100.

Cikin wadanda suka mutu da za a ba kyautar akwai tsohuwar shugabar NAFDAC, Farfesa Dora Akunyili, Dr. Stella Adadevoh da Dr. Olikoya Ransome Kuti.

Masu samun wannan lambar yabo sun kunshi shugabannin siyasa, manyan ‘yan kasuwa, kungiyoyi masu zaman kansu da suka inganta sha’anin lafiya.

Kungiyoyi suna ta ba Jonathan lambar girmamawa

A baya an ji cewa Kungiyar lauyoyi na Afrika ta zabi wasu tsofaffin shugabannin kasashe da za su yi magana a wajen babban taron da za ta yi a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Duka Ma’aikatan fadar Shugaban kasa sun dauki rantsuwar hana sirri fita daga Aso Rock

An zabi Goodluck Jonathan ya yi jawabi wajen taron AfBA, baya ga haka kungiyar za ta karrama shi. Har ila yau, AAF za ta ba Jonathan lambar yabo a bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel