Yadda muka shawo kan Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 - Janar Abdulsalami

Yadda muka shawo kan Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 - Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar ya yi bayyanin matakan da shi da wasu fitattun 'yan Najeriya suka dauka domin shawo kan tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zaben shekarar 2015.

Tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Abdulsalami Abubakar mai murabus ya yi bayani dalla-dalla yadda aka shawo kan tsohon shugaban kasa Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 wanda ya daura shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki.

A jawabin da ya yi wajen taron lauyoyin Najeriya na (NBA), tsohon shugaban ya ce shugabanin kasashen Afirka da ke kokarin sauya kundin tsarin mulki domin su dawamma kan mulki ta kowane halli sune ainihin tushen matsalar Afirka kamar yadda Tribuna ta ruwaito.

Yadda muka shawo kan Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 - Janar Abdulsalami Abubakar
Yadda muka shawo kan Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 - Janar Abdulsalami Abubakar
Asali: UGC

Abdulsalami ya yabawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bisa yadda ya amince da sakamakon zaben ba tare da wata jayaya ba da kuma halin dattaku da ya nuna ta hanyar kiran abokin hammayarsa a wayan tarho ya yi masa murnar nasarar lashe zaben.

DUBA WANNAN: An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

A cewarsa, "Ni da wasu amintattun 'yan Najeriya da masu ruwa da tsaki a fanin zaben mu zauna da 'yan takarar da shugabanin jam'iyyunsu inda muka zartar da shawarar yadda za'a kare afkuwar fitina bayan zaben.

"Mun tabbatar cewa 'yan takarar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ta fahimtar juna da kuma amincewa da sakamakon zaben tare da shawartan magoya bayansu su rungumi siyasar zaman lafiya musamman lokacin kamfe da zabe.

"Abin farin ciki ne yadda 'yan takaran biyu suka mutunta yarjejeniyar da muka sanya su suka sanya hannu a kai da kuma irin hadin kan da 'yan Najeriya suka bayar wajen gudanar da zaben na 2015.

"A bangarensa, tsohon shgaban kasa Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zaben har ma ya kira abokin hamayarsa domin taya shi murnar lashe zaben. A karshe an samu zaman lafiya da demokradiya mai dorewa a Najeriya", Inji Abdulsalami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel